Matashi ya rasa ransa a kan soyayya a Yobe
Published: 30th, October 2025 GMT
Wani matashi mai shekaru 20, Jibrin Saidu Lamido, ya rasa ransa bayan wani rikici a kan soyayya da ya auku ƙauyen Gurdadi da ke Ƙaramar Hukumar Yusufari a Jihar Yobe.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da Jibrin ya je zance wajen budurwarsa Saratu Gata, mai shekaru 22, a ƙauyen Kalameri.
Wata majiya ta ce wani mutum da ba a san ko waye ba ya zo wajensu, tare da tafiya da budurwar sannan ya ƙalubalanci Jibrin da ya biyo su idan shi “namijin gaske ne.”
Daga nan ne rikici ya ɓarke tsakaninsu, inda wanda ake zargi ya daɓa wa Jibrin adda a wuya.
“An garzaya da shi zuwa asibitin Kumaganam amma likita ya tabbatar da mutuwarsa,” in ji majiyar ’yan sanda.
Rundunar ’yan sandan jihar ta miƙa gawar mamacin ga iyayensa don yi masa jana’iza.
Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da cewa suna ci gaba da neman wanda ake zargi, wanda ya tsere bayan aikata laifin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Na’im Kassim: Idan Duniya Baki Daya Za Ta Taru, Ba Wanda Zai Iya Kwace Makaman Hizbullah
Babban sakataren kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya bayyana cewa; Amurka ta kwana da sanin cewa, za mu kare kanmu, ko da sama da kasa za ta hade.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbulllah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Babu wanda ya isa ya kwace makaman Hizbullah saboda kare manufofin Isra’ila ko da kuwa duk duniya za ta shelanta yaki akan Lebanon.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma kara da cewa: Ku saurar da kyau ku fahimta! Kasa, da makami da rai, abu ne guda daya, don haka duk wanda yake son kwace abu daya, to dukkanin wadannan guda ukun yake son kwacewa.”
Sheikh Na’im kassim ya kuma ce abinda kwace makamai yake nufi, shi ne shafe samuwarmu, ba kuwa za mu bari hakan ta faru ba.
Babban maatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce: Ba za mu taba yin ko gizau ba akan matsayarmu, domin wannan shi ne matsayi na daukaka, ba kuma da bukatuwa da shaida daga masu aikata laifuka da barna a doron kasa. Ko daga wadanda tarihinsu shi ne haddasa fitina, ko barna.”
Sheikh Na’im Kassim ya ce; Idan kun kashe mu, to jininmu da ya zuba zai tsiro.:
Haka nan kuma ya yi kira ga gwamnatin kasar ta Lebanon da ta dakatar da mika kai bori yana hawa a gaban abokan gaba.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Abu daya kawai da abokan gaba suke bukata shi ne Lebanon ta mika wuya, ta zama a karkashin ikon Isra’ila.”
Sheikh Na’im Kassim ya ce; Idan kuwa Lebanon ta mika wuya, to ta gama rushewa, domin ga Syria nan a gabanmu a matsayin misali, duk abinda yake faruwa acan yaudara ce.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka DRC: Kungiyar M23 Ta Kwace Iko Da Wani Gari Mai Muhimmanci December 13, 2025 Syria: Sojojin “Isra’ila” Sun Kutsa Cikin Yankin Qunaidhara December 13, 2025 Kalibaf: Iran Da Habasha Suna Bunkasa Alakokin Siyasa Da Tattalin Arziki December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Ziyarar Da Shugaban Rasha Ya Kai Indiya Ta Kara Karfafa Dangantakar Mosko Da Delhi December 13, 2025 Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na Venuzuela December 13, 2025 Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci