An kashe mutum 2 a rikicin limancin masallacin Juma’a a Taraba
Published: 29th, October 2025 GMT
Rikici tsakanin bangarori biyu a garin Donga na Jihar Taraba, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a kan limancin masallacin Juma’a na garin.
Bayanai sun nuna baya ga mutanen da suka mutu, wasu da dama sun jikkata kuma an lalata dukiyoyi.
An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a KadunaRikicin, kamar yadda Aminiya ta gano, ya faru ne a ranar Talata kan limancin masallacin Juma’a na garin da ke gaban fadar Sarkin Donga.
Wata majiya daga garin ta shaida wa wakilinmu cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani tsakanin kungiyoyi biyu na al’ummar Musulmi a garin kan wanda ya kamata ya zama limami na masallacin na Juma’a.
An ce sabanin ya rikide zuwa rikici mai zafi tsakanin bangarorin biyu, wanda ya haifar da mutuwar mutane biyu da kuma jikkatar wasu da dama.
Majiyar ta kara da cewa jami’an tsaro ciki har da sojoji sun isa yankin domin shawo kan halin da ake ciki.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai daga wayar ko amsa sakon da wakilinmu ya aike masa ba dangane da lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Taraba
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a Kaduna
Rikicin Jam’iyyar ADC na Jihar Kaduna ya ɗauki sabon salo, bayan da uwar jam’iyyar ta nada tsohuwar Ministar Kuɗi, Sanata Nenadi Usman, a matsayin Shugabar Hadakar Jam’iyyar a jihar.
Haka kuma jam’iyyar ta nada tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Kaduna, Bashir Sa’idu, na hannun daman tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa’i, a matsayin Mataimakin Shugaban Haɗakar.
Da yake jawabi yayin taron manema labarai, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa maso Yamma), Ja’afaru Sani, ya bayyana cewa manufar ADC ita ce haɗa kan shugabannin jam’iyyun adawa a Kaduna domin ƙarfafa dimokuradiyya da shigar kowa cikin harkokin siyasa.
Ya ce shugabannin Haɗakar sun ƙuduri aniyar sake farfaɗo da jam’iyyar da kuma haɗa kan jama’a don kawo ƙarshen abin da ya kira “mulkin danniya na Jam’iyyar APC a jihar da ƙasa baki ɗaya.”
Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro Alassane Ouattara ya lashe zaɓen Ivory Coast karo na huɗu“A bisa wannan tsari na sake gina jam’iyyar da samar da shugabanci mai tsari, mun tabbatar da naɗin Sanata Nenadi Usman a matsayin Shugabar Hadakar ADC a Jihar Kaduna, tare da Alhaji Bashir Sa’idu a matsayin Mataimakinta.
“Da wannan mataki, ita ce za ta zama ginshiƙin hada kai da shirya ayyukan Haɗakar jam’iyyar a jihar,” in ji shi.
Ja’afaru Sani ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da ƙoƙarin raba kawunan shugabannin jam’iyyun adawa a jihar, amma ya ce ADC za ta tsaya tsayin daka wajen kare haɗin kanta.
“Mun lura cewa a ƙoƙarinsu na kawo rabuwar kai, wasu ’yan siyasa da ake amfani da su sun ɗauki nauyin wasu mutane don kai ƙara kotu a kan wasu shugabannin Haɗakar, ciki har da Mallam Nasir El-Rufa’i da ni kaina,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, shugabannin Haɗakar sun cimma matsaya ɗaya ta kora da hana shiga ayyukan jam’iyya ga dukkan mambobin da ke da hannu ƙarar da aka shigar a kotu kan El-Rufa’i da sauran shugabannin jam’iyyar.