Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin Afrika
Published: 29th, October 2025 GMT
Babbar tawagar ƙwallon ƙafa ta matan Najeriya Super Falcons ta samu tikitin buga gasar cin kofin nahiyyar Afrika ta mata ta 2026 da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci.
Super Falcons ta samu nasarar ne bayan tashi kunnen doki 1 da 1 da takwararta ta jamhuriyyar Benin a filin wasa na MKO Abiola da ke birnin Abeokuta a yammacin jiya Talata.
Kunnen doki ya bai wa Najeriya nasarar shiga cikin jerin ƙasashen da zasu buga kofin na Afrika, bayan Falcons ta doke Benin da ci 2 – 0 a makon jiya a birnin Cotonou.
Hakan na nufin a wasanni biyu da ƙungiyyoyi suka fafata Najeriya ta samu nasara da ci 3-1.
Wannan dai shi ne karo na 14 da Falcons zata buga kofin nahiyyar Afrika da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci daga 17 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu na 2026.
Najeriya ta lashe gasar sau 10 cikin gasanni 14 da aka buga a tarihi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ƙwallon ƙafa ta matan Najeriya Super Falcons
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Sauya Hafsoshin Tsaro Zai Kawo Karshen Aikin Ta’dda A Najeriya?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tun bayan sauya hafsoshin tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ne dai mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu, yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen yaki da rashin tsaro, wasu kuwa na ganin duk jama’ar ja ce.
Shin ko sauya hafsoshin tsaro zai kawo karshen fargaban da al’umma ke yi?
NAJERIYA A YAU: Me Dawowar Hare-hare Kan Sojoji Ke Nufi A Arewa Maso Gabas? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari akai.
Domin sauke shirin, latsa nan