Aragchi Ya Tattauna Da Bin Salman Kan Karfafa Zumunci Tsakanin Kasashen Biyu
Published: 10th, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattaunawa da Firay minister da kuma yerma mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya Mohammad bin Salman kan karfafa dankon zumuncim tsakanin kasashen biyu da kuma abubuwan da ke faruwa a yankin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran Aragchi ya hadu da dan sarkin ne a Makka, a ranar talata , kafin haka ministocin harkokin wajen kasashen biyu wato Faisal Bin Farhan kan wadan nan batutuwan.
Bin salman dangane rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da HKI da kuma Amurka, y ace yana fatan karshensa ya zama mai samar da zaman lafiya a mai dorewa a yankin.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran ya fadawa Bin salman kan cewa kasar Iran ta gode da yadda gwamnatin saudiya ta yi allawadai da hare-haren da HKI ta kaiwa Iran a yakin 12 da suka fafata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kamfanin Sin Ya Cimma Nasarar Shimfida Layin Dogo Na Farko Dakon Kaya Mafiya Nauyi A Hamadar Afirka
Kamfanin CRCC na Sin ya cimma nasarar kammala shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 135 a jiya Litinin. Aikin ya kasance mataki na farko na shirin shimfida layin dogo na farko a hamadar Afrika, na jiragen kasa masu dakon kayayyaki mafiya nauyi, wanda zai hada jihar Bechar da yanki mai samar da karfe na Gala Jebilet a Jihar Tindouf dake yammacin kasar Aljeriya.
Gwamnan jihar Tindouf Mustapha Dahou, da babban darektan CRCC Dai Hegen sun halarci bikin kammala aiki. A gun bikin, Dahou ya ce, CRCC da jiharsa, sun yi hadin gwiwar daga matsayin layin dogon zuwa masana’antu, matakin da ya ingiza bunkasar tattalin arzikin wuri zuwa mataki na gaba. Ya kuma yi fatan bangarorin biyu za su kara hada hannu don haifar da moriyar juna da cimma nasara tare, ta yadda tattalin arziki, da zamantakewar wurin za su iya samun ci gaba mai kyau.
A nasa bangare, Dai ya ce, shirin da kamfaninsa ya ba da taimakon gudanarwa, ya shaida kwarewar kamfanin a bangaren shimfida layin dogo, kuma alama ce ta hadin gwiwar kasashen biyu. Kazalika, CRCC zai ci gaba da hadin gwiwa da Aljeriya a bangaren zirga-zirga, da makamashi, da sabbin sana’o’i da sauransu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp