Tinubu na amfani da ƙarfin mulki wajen tsoratar da ’yan adawa — Sule Lamido
Published: 23rd, July 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa.
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano.
Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a KanoLamido, ya ce hukumomi irin su EFCC ana amfani da su ne wajen matsa wa ’yan adawa lamba.
Ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin aikata almundahana.
A cewarsa bayan Okowa ya koma jam’iyyar APC, an daina tuhumarsa.
Ya kafa misali da wata magana da Sanata Adams Oshiomhole ya taɓa yi.
Ya ce: “Da zarar ka shiga APC, an yafe maka zunubanka.” (Ko da yake Oshiomhole ya musanta yin wannan magana).
Lamido, ya gargaɗi gwamnati cewa amfani da ƙarfin iko wajen azabtar da ’yan adawa zai zama barazana ga dimokuraɗiyya.
Ya ce yanzu Najeriya na fama da rashin tsaro, rarrabuwar kawuna da rashin amana, wanda shi ne abin da ya fi dacewa gwamnati ta mayar da hankali a kai.
Ya kuma soki yunƙurin da ake yi na kafa jam’iyyar haɗaka kafin zaɓen 2027.
Lamido, ya ce duk wani yunƙuri na kafa sabuwar ƙungiya ya zama wajibi ya dogara da manufofi masu amfani kamar dimokuraɗiyya, zaman lafiya, tsaro da cibgaban ƙasa, ba kawai burin mulki ko ramuwar gayya ba.
Duk da matsalolin da PDP ke fuskanta, Lamido, ya ce har yanzu yana da kishin jam’iyyar.
Amma ya ƙara da cewa, matuƙar PDP ba za ta samar da abin da ake so, zai mara wa wasu muddin hakan zai amfani ƙasa.
Game da zargin cewa yana yi wa jam’iyyar adawa aiki, Lamido ya ce: “Ina ƙoƙari ne na dawo da jam’iyyar PDP kan turbar da ta dace.”
Ya kuma zargi wasu gwamnonin PDP da yin aiki da Tinubu a ɓoye ba tare da an hukunta su ba.
Ya ce PDP sai ta dawo kan tsarin gaskiya, adalci da dimokuraɗiyya idan tana so ta dawo da ƙarfinta.
“Ƙasar nan na cikin matsala ga yunwa, talauci, da rashin tsaro sun yawaita,” in ji shi.
Game da batun ƙirƙiro sabbin jihohi, Lamido, ya ce wannan ra’ayi yana da kyau amma ba yanzu ne lokacin da ya dace a bijiro da shi ba.
Ya ce ya fi dacewa a mayar da hankali kan warware matsaloli kamar rashin tsaro da yunwa.
Da aka tambaye shi game da ziyarar jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai wa Shugaba Tinubu, Lamido, ya ce bai da abin cewa.
“Kwankwaso da Tinubu na da ‘yancin su gana. Ku tambaye shi da kanku,” in ji shi.
A ƙarshe, Lamido, ya ce mafitar Najeriya na cikin dawo da amana, gaskiya, da bin doka a harkokin siyasa da gwamnati.
“Ina tare da PDP ɗari bisa ɗari, amma idan mafita ga Najeriya tana wajen PDP, zan bi ta domin Najeriya ta fi komai muhimmanci,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Adawa Kwankwaso Tsara yunwa
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya.
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan AmurkaDon haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa.
“Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne ga ƙasarmu,” in ji Gumi.
Sheikh Gumi, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta kira Jakadan Amurka domin neman bayani da kuma a janye wannan barazanar, inda ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi haka ba, to Najeriya ta yanke hulɗa da Amurka.
“Shugaba Tinubu ya kamata ya kira Jakadan Amurka idan ba su janye barazanar ba, to mu yanke hulɗa da wannan gwamnati mara mutunci,” in ji shi.
Gumi, ya kuma jaddada cewa Najeriya tana da damar bunƙasa tattalin arziƙinta ba tare da dogaro da Amurka ba.
“Akwai hanyoyi da dama da za mu iya faɗaɗa tattalin arziƙinmu da ƙarfafa haɗin kan soji ba tare da dogaro da su ba,” in ji Gumi.