Aminiya:
2025-10-30@07:42:14 GMT

ACF ta mara wa gwamnatin Tinubu baya

Published: 30th, October 2025 GMT

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta bayyana cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.

Shugabannin ƙungiyar sun kai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, ziyara a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda suka gayyace shi zuwa bikin cika shekaru 25 da kafa ACF.

An sanya dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga kan zaɓen Tanzania Gwamnati ta bai wa ASUU N2.

3bn domin biyan bashin albashin malamai

Shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yaba da kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin Shugaba Tinubu da Shettima, ya bayyana cewa hakan alama ce ta haɗin kai da shugabanci na gari.

“A wajenmu ’yan Arewa, Mataimakin Shugaban Ƙasa shi ne jakadanmu na farko. Yana yin biyayya ga Shugaban Ƙasa kuma yana aiki tuƙuru ba don Arewa kaɗai ba, har ma da Najeriya gaba ɗaya,” in ji Dalhatu.

Dalhatu, ya ƙara da cewa ACF za ta ci gaba da mara wa gwamnati baya tare da ba ta shawarwari masu amfani a duk lokacin da ya dace.

“Muna alfahari da Mataimakin Shugaban Ƙasa da sauran ’ya’yanmu na Arewa da ke cikin gwamnati.

“Za mu ci gaba da goyon bayansu, amma kuma za mu nuna musu wuraren da ake buƙatar gyara domin amfanin dukkanin ’yan Najeriya,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ACF, wadda aka kafa a shekara ta 2000, an samar da ita ne domin haɗa kan al’ummar Arewa da kuma ƙarfafa zaman lafiya da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, ƙungiyar ta taka muhimmiyar rawa wajen magance rikice-rikice, tallafa wa ci gaban tattalin arziƙi, da kuma ƙarfafa wa matasa da al’umma gwiwa su dogara da kansu ta hanyar ilimi da sana’o’i.

Dalhatu, ya ce bikin cikar ƙungiyar shekaru 25 da kafuwa, zai zama dama ta haɗa kan ƙasa, inda za su gayyaci manyan ƙungiyoyin yankuna kamar Afenifere, Ohanaeze Ndigbo da PANDEF domin ƙarfafa zumunci da fahimtar juna.

Hakazalika, ya yi fatan bikin zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin ƙabilu Najeriya domin samun ci gaban ƙasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa kungiya Mara Baya ziyara Shugaban Ƙasa

এছাড়াও পড়ুন:

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

An bayyana cewa mahalartan EIMC 18 sun fito ne daga hukumomin tsaron Nijeriya da kuma ƙasashen Afrika kamar Chadi, Ghana, Rwanda, Somalia, da Gambiya.

 

A cikin laccarsa, Gwamna Lawal ya bayyana cewa salon Zamfara ta zama abin koyi ga sauran sassan Afrika wajen nazarin yadda ake ƙoƙarin samar da zaman lafiya da ci gaba.

 

Ya ce, “A cikin shekaru 20 da suka wuce, tsarin tsaro a Afrika ya sauya sosai. Ra’ayin cewa gwamnati ita kaɗai ke da ikon amfani da ƙarfi yanzu ya fara fuskantar kalubale daga ƙungiyoyi marasa bin tsarin gwamnati – ciki har da ‘yan sa-kai, ƙungiyoyin kare kai, ‘yan ta’adda, barayin daji da kuma cibiyoyin aikata laifuka na ƙasa da ƙasa.”

 

Gwamnan ya bayyana cewa matsalolin tsaro a Zamfara sun samo asali ne daga rashin aikin yi, taƙaddamar albarkatun ƙasa, da canjin yanayi, tare da yawaitar makamai daga rikice-rikicen yankuna.

 

Ya ce, tun da suka hau mulki a 2023, gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen kafa tsaro bisa ginshiƙai uku:

 

1. Haɗin gwiwar hukumomin tsaro ƙarƙashin kwamitin tsaro na jiha da gwamnan kansa ke jagoranta.

 

2. Ƙirƙirar Rundunar Kare Al’umma ta ‘Community Protection Guards’ (CPG) domin tallafawa jami’an tsaro.

 

3. Haɗa kai tsakanin sarakunan gargajiya, ƙananan hukumomi da hukumomin tsaro wajen raba bayanan sirri da saurin ɗaukar mataki kan barazanar tsaro.

 

Ya ƙara da cewa, an kafa kwamitocin sulhu a kowace ƙaramar hukuma da suka haɗa da sarakuna, malamai, mata da matasa domin sulhunta rikice-rikice da gina aminci.

 

Gwamnan ya ce, Zamfara na aiki tare da ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa da kuma ƙasashen ƙetare kamar Kolombiya wajen shirin Preventing and Countering Violent Extremism (PCVE) — wanda ke mayar da hankali kan shirin gyarawa da dawo da masu tubabbun ‘yan ta’adda cikin al’umma.

 

A cewarsa, “Tattaunawar sulhu na iya taimaka wajen magance rikici, amma zaman lafiya na gaskiya ba zai samu ba sai an ajiye makamai. Sulhu ba tare da iko ba dai-dai yake da miƙa wuya gare su. Barin masu bindiga da makamai yayin da ake tsara sharuɗɗan zaman lafiya hanya ce ta sake janyo tashin hankali.”

 

Gwamna Lawal ya jaddada cewa duk wani yunƙurin sulhu dole ne ya zama mai tsari, ƙarƙashin jagorancin gwamnati, tare da cikakken iko na doka. “Zaman lafiya na gaskiya yana samuwa ne idan masu ɗauke da makamai sun amince da mulkin doka, kuma gwamnati ta tabbatar tana da ƙarfin kare jama’arta.”

 

A nasa jawabin, Kwamandan Cibiyar Tsaro ta Ƙasa, J.O. Odama (FSI+, FDC), ya yaba wa Gwamna Lawal bisa hangen nesan da ya gabatar, yana mai cewa, “Ya kawo mana cikakken haske kan gaskiyar lamura a Zamfara. Na tashi a can, na san irin ƙalubalen da ya fuskanta kafin ya zama gwamna. Amma yanzu ya sauya fasalin jihar daga fuskar rashin tsaro zuwa canjin na gaskiya da kyakkyawan fata ga al’umma.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya October 29, 2025 Labarai Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC October 29, 2025 Labarai COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa  October 29, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
  • Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci
  • Gwamnatin Gombe ta fara tantance ma’aikata don kawar da na bogi
  • Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye
  • AA Zaura Ya Yi Kira Ga ’Yan Nijeriya Su Marawa Sauye-sauyen Shugaba Tinubu Baya
  • Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba
  • Alassane Ouattara ya lashe zaɓen Ivory Coast karo na huɗu
  • Sule Lamiɗo na neman takarar Shugaban PDP na Ƙasa
  • Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa