Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher
Published: 30th, October 2025 GMT
Kwamandan Runduna Kai Daukin Gaggawa ta kasar Sudan ya yi ikirarin kafa kwamitoci don binciken kisan kiyashin da aka yi a birnin El Fasher
Kwamandan Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Sudan (RSF), Muhammed Hamdan Dagalo “Hemedti,” ya amince a ranar Laraba cewa: Mayakansa sun aikata “keta haddi” a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan.
A cikin wani jawabi na bidiyo, Hemedti ya ce, “Ya ga keta haddi da aka yi a El Fasher, kuma daga nan ya sanar da kafa kwamitocin bincike, ba kawai kafa kwamitoci ba, har ma kwamitocin bincike sun riga sun isa birnin na El Fasher domin fara ayyukansu.”
Hemedti ya yi ikirarin cewa: “Kwamitocin bincike na shari’a za su fara bincike nan take da kuma daukar alhakin duk wani soja ko jami’i da ya aikata keta haddi ko laifi ga duk wani mutum da aka kama, kuma za a sanar da sakamakon binciken nan take.”
Ya kuma yi ikirarin cewa: “Yanzu an ba da izinin gudanar da zanga-zangar farar hula a El Fasher gaba daya, kuma ana sake duba batun tsare fararen hula don tabbatar da sakin su duk inda aka tsare su. Waɗannan umarni ne da za a aiwatar nan take.”
Hemedti ya bukaci mazauna El Fasher “da su koma gidajensu da matsugunansu duk da cikas da ake samu a yanzu na tashin nakiyoyi da sauran ragowar matsalolin yaki.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan. October 29, 2025 IRS: Sanya Sabbin Takunkumi Kan Kasar Iran Zai Haifar Da Mummunan Sakamakon A Yankin October 29, 2025 An saka dokar Ta Baci Bayan Barkewar Zanga-zanga A Zaben Shugaban Kasar Tanzaniya October 29, 2025 Majalisar Dattawa A Najeriya Ta Tantance Sabbin Manyan Hafsoshin Sojin Kasar October 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yi ikirarin
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan: Makaman ‘Drones’ Sun Kashe Ma’aikatan MDD 6 A Kadugli Na Kurdufan Ta Kudu
Jami’an tsaro na MDD wadanda suke aiki a rundunar (UNISFA) guda 6 ne suka rasa rayukansu a jiya Asabar a wani harin da aka kaiwa sansaninsu a lardin Kurdufan da kudu a kasar Sudan.
Shafin yanar gizo na Labarai ‘Sudan Tribune’ ya nakalto gwamnatin kasar Sudan tana aza laifin kai hare-haren kan kungiyar RSF ta yan tawaye a yankin. Amma RSF ta musanta zargin.
Dakarun MDD ta (UNISFA) dai suna tabbatar da zaman lafiya a yankin Abiea da sudan da kuma sudan ta kudu suke takaddama a kansu ne tun shekara ta 2011. Kuma wannan shi ne hari na farko kai tsaye kan dakarun MDD a yankin tun lokacinda aka fara yakin basabsa a kasar ta Sudan fiye da shekaru 2 da suka gabata. Wato tun wata Afrilun shekara ta 2023.
Labarin ya kara da cewa makaman Drones, watojiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa guda uku ne suka kai hare-hare kan sansanin sojojin na MDD inda suka kashe mutane 6 daga kasar Bangladesh suka kuma lalata wata tashar ajiyar makamashi.
Labarin ya kara da cewa mutane biyu daga cikin wadanda suka ji rauni suna cikin mummunan hali. Ya zuwa yanzu dai Majalisar bata zargi wani bangare da kai hare-haren ba. Mazauna garin Kadugli inda aka kai harin, sun bayyana cewa mayakan kungiyar SPLM-N karkashin Abdulaziz Al-Hilu sun yi barin wuta a kan garin a jiya Asabar. Bayan yiwa garin kawanyana na watanni.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Eritrea Ta Fice Daga Kungiyar Raya Kasahsen Gabacin Afrika (IGAD) December 14, 2025 َA Yau Ne Za’a Gudanar Da Taron Koli Na Kungiyar ECOWAS A Birnin Abuja December 14, 2025 Iran Ta karbi Bakunci Taron Kasashen Dake Makwabtaka Da Afghanistan Da Rasha December 14, 2025 Isra’ilaTa Kashe Wani Bafalasdine Matashi A Wani Hari Da Takai A Arewacin Kogin Jodan. December 14, 2025 Shuwagabannin Majalisar Kasar Iran Da Na Ethiopia Sun Gudanar Da Taron Manema Labarai December 14, 2025 Ghana Ta Kori Wasu Yahudawa Guda 3 Don Mayar Da Martani December 14, 2025 Araghchi ya bukaci Amurka ta girmama al’ummar Iran da gwamnatinta December 14, 2025 Dan bindiga ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula a Siriya December 14, 2025 Mutum biyu sun mutu a harbin bindiga a Jami’ar Brown ta Amurka December 14, 2025 Shugabannin kasashen (ECOWAS) na taro a Abuja December 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci