Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati
Published: 30th, October 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan zargi ya ta’allaƙa ne da bayanai marasa tushe, waɗanda ba su san yanayin tsaron Najeriya ba.
“Wasu daga cikin iƙirarin da jami’an Amurka suka yi sun dogara ne da bayanai marasa inganci da tunanin cewa yawancin waɗanda ake kai wa hare-hare Kiristoci ne,” in ji Idris.
“Waɗannan miyagu (’yan ta’adda) ba su ware addini ɗaya ba, suna kai wa Kiristoci da Musulmai hari musamman a Arewacin ƙasar nan.”
Ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai yawan addinai da ke zaune lafiya tare, kuma irin waɗannan rahotanni na ƙarya na iya haddasa rikici da tayar da fitina.
“Keɓe waɗannan hare-hare da sunan wani addini abu ne mai hatsarin gaske. Najeriya ƙasa ce wadda mutane suka yadda da juna inda mutane masu addinai daban-daban ke rayuwa cikin lumana,” in ji ministan.
Idris, ya ce gwamnati na ci gaba da inganta fannin tsaro, ciki har da samar da sabbin kayan aiki da haɗin kai mai ƙarfi tsakanin hukumomin tsaro.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2009, Najeriya ke yaƙi da ta’addanci da ’yan fashin daji, kuma sauye-sauyen da aka yi kwanan nan sauke Hafsoshin Tsaro na nufin inganta tsaro.
Ministan, ya ƙara da cewa gwamnati tana amfani da hanyoyin zaman lafiya ta hanyar noman abinci, samar da ayyukan yi, da shirye-shiryen tallafa wa jama’a don rage talauci da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Majalisar Amurka bayanai Gwamnatin tarayya Najeriya Tsaro zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 80 a Kebbi
Jami’an tsaron hadin gwiwar sun kashe fiye da ’yan bindiga 80 da suka yi yunƙurin kutsawa Jihar Kebbi ta iyakarta da Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin sama da na ƙasa sun gudanar da sumame a dajin Makuku, inda suka yi ruwan wuta kan sansanonin ’yan ta’adda, suka kuma kashe da dama daga cikinsu.
Dakarun sun kuma ceto mutane biyu da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.
A wata sanarwa da Daraktan Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kebbi, Abdulrahman Zagga, ya fitar, an bayyana cewa dakarun sun yi nasarar daƙile wani mummunan hari da sama da ’yan bindiga 400 suka kai garin Ribah, inda aka yi musu mummunar ɓarna.
An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a KadunaMai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara kan harkokin sadarwa da dabarun mulki, Abdullahi Idris Zuru, ya shaida wa manema labarai, cewa wannan aiki ya nuna tsayin daka da ƙarfin dakarun tsaro wajen yaƙi da ’yan ta’adda.
Ya ce, “Dakarun sun yi aiki tuƙuru don hana ’yan bindigar kutsawa cikin Kebbi. Wannan sumame wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin daƙile ta’addanci da fashi da makami a fadin jihar.
“Sojojin Najeriya suna ci gaba da kai hare-hare a dazuka da yankunan da ke kan iyaka, musamman a dajin Makuku.”
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar tana aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.