Abiy Ahmed: Habasha na bukatar zaman sulhu kan rikicin teku tsakaninta da Eritrea
Published: 29th, October 2025 GMT
Firayim Ministan Habasha Abiy Ahmed ya yi kira da kasashen duniya su shiga Tsakani domin yin tsakanin kasarsa da Eritrea kan batun Tekun Ja, yana mai jaddada muhimmancin kawo karshen duk wata tashin tashina a yankin Kahon Afirka.
Abiy, yayin da yake jawabi ga majalisar dokoki a Addis Ababa, ya yi watsi da batun yin amfani da karfin soja amma ya jaddada cewa dole ne a saurari bukatar Habasha, kuma a warware batun ta hanyar diflomasiyya.
“Bukatar Habasha ita ce samun damar shiga teku, amma ba mu da niyyar shiga yaki da Eritrea. Akasin haka, mun gamsu cewa za a iya warware wannan batu ta hanyar lumana da fahimtar juna ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba,” in ji Abiy.
Dangantaka tsakanin Habasha da Eritrea ta tabarbare a cikin ‘yan watannin nan, shekaru da dama bayan da Eritrea ta sami ‘yancin kai a shekarar 1993, inda ta balled aga Habasha bayan kai ruwa rana. Kasashen biyu sun yi yakin kan iyaka mai tsanani da aka zubar da jini daga 1998 zuwa 2000 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.
Duk da cewa Abiy ya sami kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2019 saboda daidaita dangantaka da shugaban Eritrea Isaias Afwerki, dangantaka ta kara yin tsami tun bayan kawo karshen yakin basasar Habasha na shekaru biyu a Tigray, inda sojojin Eritrea suka fafata tare da sojojin gwamnatin Habasha.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta kiyasta cewa rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 600,000.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hare-haren Isra’ila Sun Kashe Mutane fiye da 60 a Gaza October 29, 2025 Senegal ta sake gano wasu shaidu kan kisan gillar da aka yi a lokacin mulkin mallaka October 29, 2025 An bude taron ministocin cikin gida na kungiyar ECO October 28, 2025 Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku a Yammacin Kogin Jordan October 28, 2025 Hamas : Netanyahu Yana kokarin wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta October 28, 2025 China za ta dauki mataki idan takunkuman Iran sun shafi muradunta October 28, 2025 Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji Ukraine October 28, 2025 Pezeshkian: Hadin Kai A Tsakanin Kasashen Gabas Ta Tsakiya Ba Zabi Ba Ne, Amma Dole Ne October 28, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Waje Kan Harkokin Siyasa Na Iran Ya Ce: Iran Ba Ta Kula Da Matsin Lamba October 28, 2025 Baqa’i: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ce Ke Jagorantar Hadin Kan Iran Da Hukumar IAEA October 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dinkin Duniya Za ta Yi Zama Da Bangarorin Da ke Yaki A Sudan
Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya ce za su gana da bangarorin da ke rikici da juna a Sudan a birnin Geneva, sai dai shugaban bai bayyana ranar da za a yi wannan tattaunawar ba.
Guterres ya bayyana hakan ne a lokacin zantawarsa da kafar talabijin ta Al Arabiya da ke Saudiyya wadda ta tattauna da shi game da yunkurin da majalisar ke yi ba ganin an sasanta rikicin na Sudan.
Sai dai Tattaunawar na zuwa ne a dai dai lokacin da mayakan RSF ke ci gaba da kwace yankuna a cikin kasar tare da kisan fararen hula da dama, da kuma tilastawa miliyoyin barin matsugunansu.
Tun a tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023 ne yaki ya barke tsakanin dakarun Sojin Sudan karkashin Janar Abdelfattah al-Burhan da kuma dakarun kai daukin gaggawa na RSF karkashin Muhmmad Hamdan Dagalo ,rikicin da ya juye zuwa yaki mafi muni da kasar ta gani a tarihi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Birtaniya Ta yi Barazanar Yanke Gudunmawar Da Take Bawa Kotun Duniya December 12, 2025 Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare December 12, 2025 Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan December 12, 2025 Kungiyar NLC A Najeriya Ta Shirya Zanga-Zanga Kan Matsalar Rashin Tsaro A Fadin Kasa December 12, 2025 Duniyarmu A Yau: Iran Da Kokarin Juyin Mulkin Amurka A Yakin Kwanaki 12, Wa Ya Sami Nasara? December 12, 2025 Pezeshkian: Duniya Tana Bukatar Amintaccen Madogara, Zaman Lafiya Da Kuma Hadin Kai December 12, 2025 Iran Zata Dauki Bakoncin Taro Dangane Da Kasar Afganistan Da Tsaron Yankin December 12, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut December 12, 2025 Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba December 12, 2025 Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026 December 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci