Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP
Published: 5th, July 2025 GMT
Salim Sani Shehu
Jam’iyyar NNPP ta bayyana a hukumance cewa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai sake yin takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar a zaɓen 2027 ba.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Agbo Major, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani ga kalaman Buba Galadima, wanda ya ce Kwankwaso zai ci gaba da zama cikin jam’iyyar kuma zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027.
Major ya ce jam’iyyar ta riga ta kori Kwankwaso da Galadima bisa zargin aikata laifukan cin amanar jam’iyya, don haka ba su da ikon magana da sunan NNPP, balle su wakilci jam’iyyar a a duk wani sha’anin siyasa.
“Tun da dadewa NNPP ta sallami Kwankwaso da Galadima, don haka ba su da hurumin magana da sunan jam’iyya ko amfani da ita a wajen neman wata kujera ta siyasa,” in ji shi.
Major ya jaddada cewa babu maganar bai wa Kwankwaso tikitin takarar shugaban ƙasa kai-tsaye kamar yadda aka ba shi a zaɓen 2023, wannan karon hakan ba zai maimaitu ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kwankwaso takara Zaɓe Zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima Ya Isa Abidjan Wajen Rantsar da Shugaba Ouattara
Daga Bello Wakili
Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya isa Abidjan na kasar Côte d’Ivoire, domin wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rantsar da Shugaban Alassane Ouattara a wa’adinsa na hudu.
Za a rantsar da Shugaban ne a yau Litinin, 8 ga watan Disamban 2025, a Fadar Shugaban Kasa da ke Abidjan, wanda shugabanni daga kasashen Afrika da sauran manyan baki daga sauran kasashen duniya za su halarta.
Shugaba Ouattara ya sake lashe zabe ne a ranar 25 ga watan Oktoban 2025, inda ya sake samu wani sabon wa’adi na jagorantar kasar. Sake Rantsar da shi na nuna da ci gaban da dimokuradiyya a kasar ta Côte d’Ivoire da kuma kyakkyawar dangantakarta da Najeriya.
A cewar Fadar Shugaban Kasar, halartar Mataimakin Shugaban Kasa Shettima a taron na tabbatar da jajircewar Najeriya kan goyon bayan mulkin dimokiradiyya a yammacin Afrika. Najeriya na ci gaba da jaddada muhimmancin bin muradin jama’a da tabbatar da sauyin mulki cikin lumana a yankin.
Najeriya da Côte d’Ivoire na da kyakkyawar hulda ta aiki karkashin ECOWAS, Tarayyar Afrika, da kwamitin kasashe biyu, inda suke yin hadin gwiwa a fannoni irin su tsaro, kasuwanci, noma, yakar safarar mutane, da tattalin arzikin dijital. Dubban al’ummar ‘yan Najeriya da ke Côte d’Ivoire ma na kara zurfafa dangantakar tattalin arziki da al’adun kasashen biyu.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasa zai koma Abuja bayan kammala taron rantsarwar.