An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra
Published: 29th, October 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta ceto wata jaririya da ba ta wuce mako daya da haihuwa ba, da aka sayar kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi, tare da cafke mata huɗu da ake zargin su da hannu a cinikin.
Kakakin rundunar a jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa an samu labarin sayar da jaririyar ne a kauyen Ifite-Awkuzu da ke Karamar Hukumar Oti, inda rundunar ta ɗauki matakin gaggawa na cafke waɗanda ake zargin.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Elizabeth Okafor mai kimanin shekara 62, Esther Nweke mai shekara 48, Ngozi Maanfa mai shekara 45, da Peace Elijah Moses, wadda ita ce mafi ƙarancin shekaru a cikin su, mai kimanin shekara 25.
Ikenga ya ce binciken da rundunar ta gudanar ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifin sayen jaririyar ba tare da an tursasa su ba, kuma ba a yi masu duka ko azabtarwa ba kafin su bayyana gaskiya.
“Jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, ba ta samu wata matsala ba,” in ji Ikenga.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ikioye Orutugu, ya bayar da umarnin a mika waɗanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin ci gaba da bincike.
Ya ce bayan kammala binciken, za a gurfanar da su a gaban kotu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Anambra Satara jarirai da ake zargin
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote
Wannan tabbacin ya zo ne a daidai lokacin da farashin famfon mai ke canzawa a faɗin ƙasar, wanda tun daga kusan ₦189 a kowace lita a shekarar 2023 zuwa sama da ₦1,000, kafin ya daidaita tsakanin ₦800 da ₦900 a farkon shekarar 2025.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA