Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC
Published: 6th, July 2025 GMT
Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar Yobe, Hon. Babagana Yakubu Mohammed, ya ajiye muƙaminsa na mai taimakawa gwamna na musamman ya kuma fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC.
Babagana, ya sanar da ajiye aikin nasa ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali.
Ba Ni Da Niyyar Barin APC Zuwa Wata Jam’iyyar — Gwamna Zulum Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata NatashaA kwafin wasiƙar da LEADERSHIP ta samu, Babagana ya bayyana matuƙar damuwarsa kan yadda aka yi watsi da wanda suke hidimtawa gwamnati da taimaka mata.
A ƙarshe, ya godewa gwamna Buni bisa damar da ya ba shi na yin aiki a gwamnatinsa, tare da yi masa fatan alheri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA