Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON ta yi kira ga jihohin kasar nan da su yi koyi da Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa wajen tare kujerun aikin hajji domin baiwa Maniyatan su damar sauke farali.

Kwamishina a hukumar mai kula da shiyyar arewa maso yamma , Sheikh Muhammad Bin Usman yayi wannan kiran a lokacin da ya kai ziyarar aiki a Dutse, babban birnin Jihar.

Sheikh Muhammad Bin Usman yayi bayanin cewar, ya zama wajibi ga sauran hukumomin Alhazan kasar nan da su yi koyi da Gwamna Umar Namadi wajen bai wa hukumomin Alhazai bashin kudade domin tare kujerun aikin Hajji ga maniyata.

Yana mai nuni da cewar, a halin yanzu, jihar Jigawa ce ta farko wajen biyan kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan.

Babban malamin ya kuma yabawa Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa namijin kokarin sa wajen shirye shiryen aikin Hajji akan lokaci.

Da ya waiwayi batun hadaya kuma, Sheikh Bin Usman yace a duk fadin kasar nan, jihar Jigawa ce take da lasisin yin Hadaya ga maniyata.

Ya ce ita kadai ce tilo take samarwa da maniyatan ta masauki a kusa da harami sabanin wasu hukumomin alhazai da suke yayatawa.

A na shi jawabin, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce wannan shi ne karo na uku da Gwamna Umar Namadi ke bai wa hukumar rancen kudi domin tare kujerun aikin hajji.

Ya ce makasudin bada rancen kudaden shi ne domin bai wa maniyatan jihar damar sauke farali.

A don haka, Labbo yace tuni hukumar ta ci gaba da rijistar maniyatan aikin Hajjin 2026 tare da bada tabbacin hukumar na ci gaba da rike kambunta wajen gabatar da aikin hajjin.

Kazalika, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya shawarci sauran hukumomin Alhazai su kara himma wajen biyan kudaden kujerun da aka ware musu akan lokaci.

Ya kuma yaba wa NAHCON da Gwamnatin jihar bisa hadin kai da goyon bayan da suke baiwa hukumar a kowanne lokaci.

 

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa jihar Jigawa Jihar Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona

 

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin October 28, 2025 Daga Birnin Sin An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas October 28, 2025 Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Gwarzo Ta Karfafa Yaƙi Da Miyagun Kwayoyi Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
  • Majalisar Dokokin Kano Ta Ce An Yi Rashin Adalci Wajen Ɗaukar Aikin Kwastam A Nijeriya
  • Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
  • Gwamnatin Gombe ta fara tantance ma’aikata don kawar da na bogi
  • Zamfara Ta Fara Sauyawa Zuwa Jihar Fasahar Zamani, In ji Gwamna Lawal
  • Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona
  • Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi
  • An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa
  • Mutanen Katsina Sun Koka Kan Dakatar da Aikin Gyaran Hanyar Mararrabar Kankara–Dutsinma–Katsina