Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno
Published: 29th, October 2025 GMT
Habiba Abubakar mai shekaru 35 da ’yarta Adama mai shekaru 9 sun rasa rayukansu bayan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Karamar Hukumar Hawul da ke Jihar Borno.
Mai magana da yawun Rundunar ’San Sanda ta jihar, Nahum Daso, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 1:15 na rana, yayin da suke komawa gida daga gona.
Ya ce, “Sun fito daga gona ne kuma suna ƙoƙarin ketare wani kogi da ke kusa da kauyen Ghung. Amma saboda ƙarfi da saurin ruwan, jirgin ruwan nasu ya kife a wani wuri mai zurfi na kogin.”
A cewarsa, jami’an ’yan sanda tare da masu aikin ceto a yankin daga bisani sun gano gawarwakin su daga cikin kogin.
“Ba a ga wata alama ta tashin hankali a jikin gawarwakin ba. An ɗauki hotuna don adana bayanai kafin a kai su Asibitin Garkida da ke Karamar Hukumar Gumbi a Jihar Adamawa, domin shi ne asibitin da ya fi kusa da su,” in ji Daso.
An mika gawarwakin ga iyalansu don yin jana’izar su bisa tsarin Musulunci.
“A halin yanzu, Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan jihar da ke Maiduguri ya fara bincike kan lamarin,” in ji Daso.
Aminiya ta ruwaito cewa a watan Satumba an gano gawar wani yaro mai sayar da kaya, wanda ake kyautata zaton ya kai shekaru 12, daga cikin kogin Gamboru da ke unguwar Customs a birnin Maiduguri, babban birnin jihar.
A ’yan watannin nan dai ana samun yawan nitsewar jiragen ruwa musamman a yankin Arewa maso Gabas na ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hatsarin Jirgin Ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
Ya ce, wanda ake kara ya nema kuma an bashi kudin fansa har Naira miliyan 15 daga iyalan wanda aka kashe kafin su kashe shi.
“Sun bugi wanda aka kashe a kai da ƙirji da sanda sannan daga baya suka binne gawar a gidan Adamu da ke Dawakin Kudu,” in ji mai gabatar da kara ga kotun.
Da take yanke hukunci, Mai Shari’a Aisha Mahmoud ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da hujjoji game da karar da suka shigar a kan Adamu ba tare da wata shakka ba.
“Ina yanke wa Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya buga wa wanda aka kashe sanda a kansa da ƙirjinsa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Ubangiji ya yi masa rahama,” in ji ta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA