Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu
Published: 30th, October 2025 GMT
Isra’ila ta kai hare-hare da dama a safiyar Alhamis kan yankunan gabashin Khan Younis, a kudancin Zirin wanda ke nuna yadda isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
A cewar kafofin watsa labaran Falasdinawa, sama da hare-hare 10 a jere Isra’ila ta kai.
Bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna makamai masu linzami na dira akan wuraren zama a gabashin birnin.
A lokaci guda, tankunan yaki na Isra’ila da motocin sulke sun yi ruwan bama-bamai a yankunan zama a gabashin Gaza.
Sojojin Isra’ila sun kuma lalata gidaje da dama a gabashin birnin Gaza. Kasa da awa daya bayan haka, sojojin gwamnatin sun sake kai hari kan gidajen fararen hula a wannan yanki.
Hakazalika, sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hari kan yankunan arewa maso gabashin Khan Younis, da kuma unguwannin Ma’an, Sheikh Nasser, da Joura al-Lout a kudancin birnin.
Wannan mummunan harin sama ya biyo bayan wani mummunan harin bam da ya kashe mutane sama da 109, ciki har da akalla yara 52, a fadin yankin Falasdinawa da yaki ya daidaita.
Hamas ta zargi gwamnatin Sahyoniya da karya yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kungiyar ta yi kira ga bangaroron da suka shiga tsakani a yarjejeniyar tsagaita wutar, wato Masar, Qatar, Turkiyya da Amurka, da su dauki mataki nan take don matsa lamba ga gwamnatin isra’ila.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar MDD Ta Musamman A Falasdinu Ta Soki Shirin Trump Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza
Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu ta soki shirin Trump kan Gaza tana mai jaddada cewa: “Yana daga mafi munin cin mutuncin da ta taɓa gani a rayuwarta
Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman kan Kare Haƙƙin Dan Adam a Yankin Falasɗinu, Francesca Albanese, ta bayyana shirin zaman lafiya na Shugaban Amurka Donald Trump a Gaza a matsayin “mafi munin cin mutunci da na taɓa gani a rayuwarta,” tana mai tabbatar da cewa Shirin ba shi da haƙƙi na shari’a da na ɗabi’a.
Albanese ta bayyana cewa: Ba ta da imani da tsarin siyasa na yanzu da ake Shirin aiwatarwa a Gaza ba, tana mai ƙarawa da cewa, “Ba za a iya gina yarjejeniyar zaman lafiya bisa karya dokokin ƙasa da ƙasa ba, kuma ba ta amince da mutanen da ke da alhakin gudanar da wannan tsari ba.” Tana mai nuni da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ba ta son ci gaba da zaman Falasɗinawa a Gaza, tana mai bayyana cewa wannan matsayi ya kasance bayyananne tsawon shekaru, a cewarta a wata hira da jaridar iPaper ta Birtaniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Isra’ila Na Kai Hare-Hare Kan Gaza A Matsayin Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 29, 2025 Larijani: Dangantakar Iran da Pakistan na iya komawa babban hadin gwiwa a tsakaninsu October 29, 2025 Iraki: Al-Sudani ya kirayi Irakawa da suka kare kundin tsarin Mulki ta hanyar fitowa zabe October 29, 2025 Abiy Ahmed: Habasha na bukatar sulhu kan rikicin teku tsakaninta da Eritrea October 29, 2025 Hare-haren Isra’ila Sun Kashe Mutane fiye da 60 a Gaza October 29, 2025 Senegal ta sake gano wasu shaidu kan kisan gillar da aka yi a lokacin mulkin mallaka October 29, 2025 An bude taron ministocin cikin gida na kungiyar ECO October 28, 2025 Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku a Yammacin Kogin Jordan October 28, 2025 Hamas : Netanyahu Yana kokarin wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta October 28, 2025 China za ta dauki mataki idan takunkuman Iran sun shafi muradunta October 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci