HausaTv:
2025-10-15@05:43:07 GMT

Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahadi A Wani Hari Na HKI

Published: 5th, July 2025 GMT

Rahotanni daga kudanci Lebanon sun ce, sau uku jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a kan gidajen mutane da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu da dama.

A garin Shaqra’dake yankin Bint-jubail, jiragen sama marasa matuki sun kai hare-hare da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu da raunuka, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar.

Har ila yau wani jirgin maras matuki na abokan gaba ya kai wani harin akan wata mota a yankin “Safful-Hawa” da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya.

A garin Shab’a kuwa ‘yan sahayoniyar sun kai hari akan wani gida, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar mutanen dake cikinsa.

Majiyar asibiti a garin Marja’iyyun ta ce an kai mata wani mutum wanda ya sami raunuka masu hatsari.

HKI dai tana ci gaba da kai hare-hare akan kasar Lebanon bayan tsagaita wutar yaki a shekarar da ta gabata.   

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ya yi sanadiyyar

এছাড়াও পড়ুন:

Rasha ta kai wa tawagar kayan agajin MDD hari a Ukraine

Rasha ta kai harin jirage kan ayarin kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a makwabciyarta kasar Ukraine da suka fi shekara biyu suna yaki.

Hukumomin Ukraine sun dakarun soji da ke yankin kudancin Kherson da suka mamaye a Ukraine ne suka kai harin a ranar Talata, inda suka lalata motocin Shirin Abinci na Duniya, a yayin da ma’akatan agajin suka shafe kimanin awa hudu ba su motsa ba saboda luguden bamabaman.

Kwamandan hukumar soji da ke yankin ta bayyana cewa an kona motoci hudu tare da lalata wata a cikin tawagar kayan agajin, amma ba a samu asarar rayuka ba a harin da aka kai da jirage marasa matuka da manyan bindigogin atilare a garin Bilozerka.

Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andriy Sybiga ya bayyana harin a matsayin “wani mummunan karya dokokin kasa da kasa, wanda ke tababtar da cewa Rasha ba ta mutunta rayukan fararen hula da nauyin da ya rataya a wuyanta na kasa da kasa.”

Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Issa Bakary Tchiroma ne ya lashe zaɓen Kamaru —’Yan adawa

Kawo yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ko Rasha ko Amurka ba su ce uffan kan lamarin ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta
  • ’Yan bindiga sun kai hari a Kankia
  • An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa
  • Rasha ta kai wa tawagar kayan agajin MDD hari a Ukraine
  • Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata
  • Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan
  • Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin  Gargadi A Kasa Baki Daya .
  • Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi 
  • Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
  • Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon