Tinubu ya ƙirƙiri sabon harajin da zai iya ƙara N100 a kan kowacce litar man fetur
Published: 30th, October 2025 GMT
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar da sabon harajin shigo da kaya na kashi 15 cikin 100 kan dukkan man fetur da dizil din da aka shigo da shi zuwa Najeriya.
An tsara wannan mataki ne domin kare matatun man cikin gida da kuma daidaita kasuwar man fetur a ƙasa, sai dai ana sa ran hakan zai iya haifar da ƙarin farashin man a gidajen mai.
A cikin wata wasiƙa da aka rubuta a ranar 21 ga Oktoba, 2025, kuma aka bayyana a hukumance a ranar 30 ga Oktoba, 2025, zuwa Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS) da Hukumar Kula da Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA), inda Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin aiwatar da harajin nan take a matsayin wani ɓangare na tsarin harajin shigo da kaya da gwamnati ta bayyana a matsayin “tsarin da ke daidaita da kasuwa.”
Wasiƙar, wacce Sakataren Shugaban Ƙasa, Damilotun Aderemi, ya sanya wa hannu, ta nuna amincewar Shugaban bayan da Shugaban Hukumar FIRS, Zacch Adedeji, ya gabatar da shawararsa.
Shawarar ta nemi a fara amfani da harajin kashi 15 cikin 100 kan kuɗin kaya, inshora da jigilar man fetur da dizal da ake shigo da su, domin daidaita farashin shigo da kaya da yanayin kasuwar cikin gida.
A cikin takardar da ya aike wa Shugaban Ƙasa, Adedeji ya ce wannan mataki na daga cikin gyare-gyaren da ake ci gaba da aiwatarwa domin ƙarfafa matatun cikin gida, tabbatar da daidaiton farashi, da kuma ƙarfafa tattalin arzikin man fetur da ke dogaro da naira.
“Babban burin wannan tsari shi ne aiwatar da cinikayyar danyen mai da naira, ƙarfafa matatun cikin gida, da kuma tabbatar da wadataccen man fetur mai arha a fadin Najeriya,” in ji Adedeji.
Shugaban FIRS ya kuma yi gargaɗin cewa rashin daidaito tsakanin farashin kayayyakin da ake tacewa a cikin gida da farashin da ake amfani da shi wajen ƙayyade farashin gidajen mai na shigo da kaya ya janyo rashin tabbas a kasuwa.
A cewar hasashen da ke cikin wasiƙar, harajin kashi 15 cikin 100 zai iya ƙara farashin saukar man fetur da kimanin Naira 99.72 a kowace lita.
Wannan sabon mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke ƙara ƙoƙari don rage dogaro da shigo da man fetur da dangoginsa daga ƙasashen waje, tare da ƙarfafa tacewa a cikin gida.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Haraji shigo da kaya
এছাড়াও পড়ুন:
Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II
“Ba za mu ci gaba da ɓata kuɗi a kan abubuwan banza ba, kamar yawan ministoci, sayen motocin gwamnati, da ma’aikatan da ke yi wa shugabanni hidima.
“Idan muna samun ƙarin kuɗi amma muna kashe su ba daidai ba, to duk ci gaban da muka samu ba zai yi tasiri ba,” in ji shi.
Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce matsalolin tattalin arziƙin Nijeriya sun samo asali ne shekaru da dama.
Ya shawarci shugabanni su riƙa sauraron masu faɗa musu gaskiya maimakon waɗanda ke yabonsu kawai.
Ya kuma tunatar da ‘yan Nijeriya cewa da an cire tallafin man fetur tun wuri da ha rage wahalar da ake ciki yanzu, amma gwamnatocin baya sun kasa samun ƙarfin gwiwar yin hakan.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA