An sanya dokar hana fita bayan ɓarkewar zanga-zanga kan zaɓen Tanzania
Published: 30th, October 2025 GMT
An sanya dokar hana zirga-zirgar jama’a a Dar es Salaam, babban birnin Tanzania, bayan da ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsarin gudanar da zaɓen ƙasar.
Bayanai sun ce masu zanga-zangar sun riƙa yaga hotunan Shugaba Samia Suluhu Hassan tare da ƙona wani ofishin ’yan sanda, yayin da suke zargin cewa akwai son kai da rashin gaskiya na fifita jam’iyya mai mulki, tare da neman gwamnati ta gyara tsarin zaɓe da kuma ba kowa damar faɗar albarkacin baki.
Zanga-zangar dai ta ɓarke ne yayin da ake tattara sakamako bayan kammala kaɗa ƙuri’a a zaɓen na yau Laraba da manyan ’yan takarar adawa walau suke ɗaure ko kuma aka hana su takara baki ɗaya.
Duk da sojoji da tankokin yaƙi da aka jibge a Dar es Salaam da wasu muhimman wurare, ɗaruruwan matasa sun fita tituna suna rera waƙoƙin cewa “muna buƙatar maido mana da ƙasarmu,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Haka kuma wata ƙungiya da ke sa ido kan harkokin Intanet mai suna NetBlocks ta ce an katse layukan sadarwa a fadin ƙasar.
Rahotanni sun ce mutane ba su fito da yawa ba a rumfunan zabe sabannin zabukan baya.
Ana dai sa ran Shugaba Samia Suluhu Hassan ce za ta lashe zaɓen domin yin tazarce a wa’adin mulki karo na biyu.
Samia Hassan ta hau kan mulki daga matsayin mataimakiyar shugaban ƙasa a shekarar 2021 bayan rasuwar wanda ya gabace ta, John Magufuli.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Juventus ta kori kocinta Igor Tudor
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta kori kocinta, Igor Tudor, bayan da ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki biyar kacal a wasanni biyar da ta buga a baya-bayan nan.
A cewar wata sanarwar da kulob ɗin ya fitar a ranar Litinin, Massimiliano Brambilla, wanda shi ne kocin tawagar maza ta farko, zai jagoranci Juventus a wasan da za ta kara da Udinese a ranar Laraba.
An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba“Juventus FC na sanar da cewa ta sallami Igor Tudor daga matsayin kocin tawagar maza ta farko, tare da sauran jami’ansa da suke taimaka masa a aikin horarswa — Ivan Javorcic, Tomislav Rogic da Riccardo Ragnacci,” in ji sanarwar.
Kulob ɗin ya gode wa Tudor da tawagarsa bisa kwazon da suka nuna a watannin da suka jagoranci kungiyar, yana yi musu fatan alheri kan duk lamuransu a nan gaba.
Yanzu haka Juventus tana mataki na takwas a teburin Serie A, da tazarar maki shida tsakaninta da Napoli wadda ke jan ragamar gasar.
A kofin Zakarun Turai na Champions League kuwa, Juve na matsayi na 25 cikin ƙungiyoyi 36 bayan ta yi canjaras ɗaya da kuma shan kashi a wasanni biyu na farko.
Tudor, tsohon ɗan wasan tsakiya na Croatia mai shekara 47, ya buga wasa da Juventus a lokacin yana murza leda, inda a watan Maris na bana kuma ya karɓi ragamar kulob ɗin daga hannun Thiago Motta.
Tun daga ranar 10 ga Satumban bana, Juventus ta buga wasanni takwas ba tare da samun nasara ba, ciki har da wasanni huɗu na bayan nan da ba ta zura ƙwallo ko ɗaya ba.
Alƙalumma sun nuna cewa Tudor ya samu nasara a wasanni 10 da ya jagoranci Juventus, sannan ya yi canjaras 8, da shan kashi sau shida.
Rahotanni na cewa wannan dai shi ne yanayi mafi muni da kulob ɗin ya fuskanta a baya-bayan nan, duk da cewa ya kashe euro miliyan 130 wajen cefanen ’yan wasa.
Daga cikin sabbin ’yan wasan da Juventus ta saya akwai Francisco Conceição, Nico González, Edon Zhegrova, da masu tsaron baya — Lloyd Kelly da Piere Kalu. Sai kuma Loïs Openda da ta ɗauko aro da Jonathan David da kulob ɗin ya ɗauko kyauta.