Sojojin Isra’ila Na Kai Hare-Hare Kan Gaza A Matsayin Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
Published: 29th, October 2025 GMT
Falasdinawa da dama ne suke ci gaba da yin shahada sakamakon ci gaba da kai hare-hare kan Zirin Gaza da Yahudawan Sahayoniyya ke yi
An kashe fararen hula Falasdinawa da dama, wasu kuma sun jikkata yayin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren sama a yankin Gaza tun jiya da daddare, wanda hakan keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne.
Majiyoyin lafiya sun ruwaito cewa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 65 tun jiya da daddare har zuwa wayewar gari a yau Laraba, ciki har da 18 daga birnin Gaza da arewacin yankin Gaza, 40 daga tsakiyar yankin Gaza, da kuma 7 daga Khan Younis.
Majiyoyin yankin sun ruwaito cewa jiragen yakin sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wani tanti a sansanin ‘yan gudun hijira na Insan da ke gabashin Asibitin Shahidai na Al-Aqsa da ke Deir al-Balah, inda suka kashe Falasdinawa biyar: Islam al-Batrighi, Omar Subhi Rubi, da ‘ya’yansa biyu, Awais da Raseel, da Shaimaa Sami Rubi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Larijani: Dangantakar Iran da Pakistan na iya komawa babban hadin gwiwa a tsakaninsu October 29, 2025 Iraki: Al-Sudani ya kirayi Irakawa da suka kare kundin tsarin Mulki ta hanyar fitowa zabe October 29, 2025 Abiy Ahmed: Habasha na bukatar sulhu kan rikicin teku tsakaninta da Eritrea October 29, 2025 Hare-haren Isra’ila Sun Kashe Mutane fiye da 60 a Gaza October 29, 2025 Senegal ta sake gano wasu shaidu kan kisan gillar da aka yi a lokacin mulkin mallaka October 29, 2025 An bude taron ministocin cikin gida na kungiyar ECO October 28, 2025 Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku a Yammacin Kogin Jordan October 28, 2025 Hamas : Netanyahu Yana kokarin wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta October 28, 2025 China za ta dauki mataki idan takunkuman Iran sun shafi muradunta October 28, 2025 Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji Ukraine October 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila
Ghana ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin cin mutuncin ‘yan kasarta a filin jirgin sama na Ben Gurion na Isra’ila, bayan da aka tsare wasu fasinjoji ko kuma aka yi musu korar kare, ta kuma ce tana tunanin daukar irin wannan matakin na ramuwar gayya.
Ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa, ‘yan kasar bakwai da suka hada da ‘yan majalisar wakilai hudu, an tsare su ba tare da wani dalili ba, kuma an sake su ne bayan shafe sa’o’i masu yawa ana tatatunawa ta shiga tsakani na diflomasiyya, yayin da aka kori wasu uku.
Tawagar majalisar ta kasance tana halartar wani taron kasa da kasa kan harkokin tsaro ta yanar gizo a Tel Aviv, yayin da fasinjoji ukun da aka kora a ka tasa keyarsu zuwa Ghana.
Sanarwar ta kara da cewa, “wannan dabi’a ta cin mutunci na mahukumomin Isra’ila abu ne mai matukar tayar da hankali kuma ba za a amince da shi ba,” ta kara da cewa “Ma’aikatar harkokin wajen kasar za ta gayyaci jami’an ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Accra domin mika musu sako na nuna bacin rai da kakkausar murya.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, “Ikrarin gwamnatin Isra’ila na cewa ofishin jakadancin Ghana ya gaza bayar da hadin kai wajen mayar da ‘yan kasar, kwata-kwata ba shi da tushe,” ta kara da cewa “aikin da jami’an Ghana suka yi a Tel Aviv ya kasance mai daukar hankali tare da bin dokokin kasa da kasa.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci