Trump Ya Kakabawa Wata Jami’in MDD Takunkumi Bayan Ta Fallasa Laifukan HKI Da Hannun Amurka A Ciki
Published: 10th, July 2025 GMT
Gwamnatin kasar Amurka ta dorawa wata ma’aikaciyar MDD takunkumi saboda yadda take amfanin laifukan yaki da take yi a gaza da kuma irin tallafin da Amurka take bawa HKI yasa tana da hannun a kissan kiyashin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa shi ya sa hannu a kan umurnin takunkuman da aka dorawa Francesa Albanese, jami’a mai kula da tattara bayanai na musamman a kan Falasdinu ga hukumar kare hakkin bil’dama da MDD.
Rubio ya bayyana cewa sanadiyyar rahoton ta ne kotun ICC ta fidda samacin kama Banyamin Natanyaho, da kuma tsohon ministansa na Tsaro Yoav Galant. Banda haka takan bada rahoto kan yadda Amurka da wasu kasashen yamma suke aikawa HKI makamai.
Sannan ya ce: Albanese tana yawan amfani da Kalmar kissan kiyashi a rahotonta. A watan da ya gabata ta bukaci a sanyawa HKI takunkuman tattalin arziki mai tsanani. A wani lokacin kuma ta bukaci majalisar ta kori HKI daga MDD.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Tana Tana Son Ci Gaba Da Yaki Kuma Trump Yana Tare Da Shi
Wata majiya wacce bata son a bayyana sunanta a nan Iran ta fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa a ziyarar da Benyamin Natanyaho yake yi a halin yanzu a kasar Amurka ya nuna cewa yana son ci gaba da yaki da kasar Iran sannan da alamun shugaba Trump yana tare da shi.
Labarin ya kara da cewa matsayin shuwagabannin biyu a yanzun bai da bambanci da matsayinsu bayan yakin kwanaki 12.
Majiyar ta bayyaa cewa Iran a shirye take ta kare kansa, kuma tana ganin ziyarar da Natanyahu yake a Amurka duk yaudara ce, saboda tuni sun rika sun yanke shawara kan ci gaba da yaki.
Dangane da sake dawowa kan teburin tattaunawa da Amurka kuma, majiyar ta ce, Idan Trump yana ganin da sauki zamu sake komawa kan teburin tattauna da shi, yana ruda kansa ne.