Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye
Published: 29th, October 2025 GMT
Gwamnatin kasar Kamaru ta ce za ta dauki matakin shari’a kan babban jagoran adawar kasar, Issa Tchiroma Bakary, bisa zarginsa da tayar da tarzoma bayan zaben shugaban ƙasa.
Ministan cikin gida na kasar, Paul Atanga Nji, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai suka nuna.
Ya ce hukumomin kasar sun fara tattara saƙonnin kafafen sada zumunta da bidiyo da aka bayyana a matsayin “ƙarya” da kuma masu tayar da hankali domin a gurfanar da masu wallafa su a gaban kotu, “kamar yadda ɗan takara Issa Tchiroma da abokan aikinsa ke da alhakin shirin tayar da tarzoma da nufin jefa ƙasar cikin rudani,” in ji Nji a taron manema labarai da aka gudanar a Yaoundé, babban birnin kasar.
Sakamakon zaben da Majalisar Dokoki ta ƙasa ta bayyana a ranar Litinin ya nuna cewa Shugaba Paul Biya ya sake lashe shi da kaso 53.66 cikin 100 na ƙuri’u, inda ya samu wa’adin mulki na takwas.
Hakan dai na nufin zai ci gaba da shugabanci na shekaru 43, kuma zai kasance matsayin shugaban ƙasa mafi dadewa a kan karagar mulki a duniya.
Issa Tchiroma ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 12 ga Oktoba.
Magoya bayansa, da suka amsa kiran yin zanga-zanga a ranar Lahadi, sun yi taho-mu-gama da jami’an tsaro kafin sanar da sakamakon, lamarin da ya haifar da mutuwar akalla fararen hula hudu.
Nji ya ce duk da wasu ƙananan rikice-rikice da aka samu, an samu daidaito a fannin tsaro, yana mai cewa an kammala dukkan tsarin zabe bayan sanarwar sakamakon da Majalisar Dokoki ta fitar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Issa Tchiroma Bakary Kamaru Paul Biya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Gudanar Da Taron Tunawa Da Kisan Kiyashin Nanjing
Cikin makwanni shida, dakarun na Japan sun hallaka Sinawa fararen hula, da sojoji da ba sa dauke da makamai kimanin 300,000, a wata ta’asa mafi muni da ta auku yayin yakin duniya na biyu.
Memban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Shi Taifeng, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin na sa, ya yi kira ga daukacin Sinawa da su zage-damtse wajen ingiza farfado da kasa, da bayar da gagarumar gudummawa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaban bil’adama. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA