Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin
Published: 30th, October 2025 GMT
Killace Gaza da gwamnatin mamayar Isra’ila take ci gaba da yi tun bayan tsagaita bude wuta ya yi sanadiyyar mutuwar masara lafiya 1000 a yankin
Majiyoyin lafiya na Falasdinawa sun tabbatar a yau Alhamis, 30 ga watan Oktoban shekara ta 2025 cewa: Tun bayan tsagaita bude wuta, gwamnatin mamayar Isra’ila ta hana shigar da kayan aikin likita da kayayyakin bukatu cikin Gaza, yayin da marasa lafiya dubu suka mutu sakamakon tsauraran matakan tsaro da kuma rufe hanyoyin shiga cikin yankin.
Majiyoyin sun bayyana cewa kashi 10% ne kawai na bukatun lafiya suka shiga yankin Gaza, kuma babu na’urorin MRI masu aiki a yankin Gaza.
Dr. Muhammad Abu Salmiya, Darakta Janar na Al-Shifa Medical Complex, ya bayyana cewa tun bayan karshen yakin, kashi 10% ne kawai na bukatun suka shiga yankin, kuma Gaza na rasa adadi mai yawa na marasa lafiya a kowace rana saboda hana kayayyakin magunguna shiga yankin.
Dr. Abu Salmiya ya bayyana fargabarsa game da yaduwar ƙwayoyin cuta a yankin, yana mai lura da cewa marasa lafiya 350,000 suna buƙatar magani don magance cututtuka masu tsanani, waɗanda magunguna an hana shigarsu Gaza, yayin da adadin masu fama da asma ya ƙaru saboda tarkace a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan. October 29, 2025 IRS: Sanya Sabbin Takunkumi Kan Kasar Iran Zai Haifar Da Mummunan Sakamakon A Yankin October 29, 2025 An saka dokar Ta Baci Bayan Barkewar Zanga-zanga A Zaben Shugaban Kasar Tanzaniya October 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe mai ciki da ɗanta a Kano
Al’ummar unguwar Sheka Sabuwar Gandu da ke Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano, sun shiga fargaba, bayan wasu da ba a san ko su waye ba, suka kashe wata mai ciki da ɗanta ɗan wata18 a duniya.
An tabbatar da faruwar lamarin da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da mijin matar ya dawo gida daga aiki ya tarar ƙofar gidan a kulle.
Hafsan sojin ƙasa ya buƙaci sabbin dakaru su zama masu kishin ƙasa An kashe mutum 11 da jikkata wasu 29 a bikin Yahudawa a OstireliyaA cewar maƙwabtan matar, bayan mijin ya tambayi jama’a a unguwar, sai ya shiga gidan, inda ya tarar da gawar matarsa da ta ɗanta.
Daga nan ne al’ummar unguwar suka sanar da hukumomin tsaro.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban jama’a aunguwar, Ahmad Sani, ya ce jama’a sun shiga firgici da tashin hankali matuƙa.
Ya koka da rashin tsaro a yankin, inda ya bayyana cewa duk da gina ofishin ’yan sanda a unguwar, har yanzu ba a turo jami’an tsaro da za su kula da shi ba.
“Dukkanin al’ummar unguwar sun shiga ruɗani. Ba a taɓa samun irin wannan abu ba. Muna cikin damuwa saboda babu jami’an tsaro a nan,” in ji shi.
Ya roƙi Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, da ya ɗauki matakin gaggawa wajen inganta tsaro a yankin domin hana sake faruwar hakan.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba zai ce komai ba domin rundunar na gudanar da bincike.
A halin yanzu, mazauna yankin sun buƙaci hukumomin tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata laifin.