Leadership News Hausa:
2025-10-30@22:22:19 GMT

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Published: 30th, October 2025 GMT

Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai

Shugaba Bola Tinubu ya yi wa sabbin Shugabannin Sojoji ado da karin girma domin su dace da sabbin muƙamansu. Sabbin shugabannin rundunar sojin kasar da aka yi wa ado sun hada da Laftanar Janar, wanda yanzu ya zama Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, a matsayin Babban Hafsan Tsaro (CDS); da kuma Manjo Janar yanzu ya koma Laftanar Janar Emmanuel Undiendeye Undiendeye a matsayin Babban Hafsan Tsaro na farin kaya (CDI).

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda  Sauran su ne Manjo Janar, wanda yanzu ya zama Laftanar Janar Waidi Shaibu a matsayin Babban Hafsan Soja (COAS); Air Vice Marshal, wanda yanzu ya zama Air Marshal Kevin Aneke a matsayin Babban Hafsan Sojan Sama; da kuma Rear Admiral, wanda yanzu ya zama Vice Admiral Idi Abbas a matsayin Babban Hafsan Sojan Ruwa. Shugaba Tinubu ya sanar da maye gurbin Shugabannin Rundunar tsaron ne a ranar Juma’ar da ta gabata, wani mataki da aka danganta da bukatar sake mai da hankali da kuma karfafa tsaron kasa. Bayan haka, Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin Shugabannin Rundunar tsaron da su dauki mataki mai tsauri kan barazanar tsaro da ke tasowa a fadin kasar, yana mai gargadin cewa ‘yan Nijeriya na tsammanin ganin sakamako, ba uzuri ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda  October 30, 2025 Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai October 30, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: a matsayin Babban Hafsan wanda yanzu ya zama

এছাড়াও পড়ুন:

Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa, wata gobara ta ƙone wani shagon Adidas Sports da ke cikin rukunin babban kantin nan na sayar da kayayyaki na Jabi Lake Mall, Abuja da tsakar daren Alhamis.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shagon ne kaɗai gobarar ta shafa.

An kuma samu rahoton cewa, an baza jami’an kashe gobara daga Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da na Kamfanin Berger da na hukumar kashe gobara ta Abuja da kuma jami’an ’yan sanda zuwa wurin.

Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29

A lokacin da Wakilin Daily Trust ya kai ziyara da safe zuwa wurin, an shawo kan gobarar.

Wani ma’aikaci a shagon ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na tsakar daren ranar Alhamis.

Ya ce, ba a samu asarar rai ba a wurin. Ya kuma tabbatar da cewa, “Shagon sayar da kayan Wasannin Adidas ne kawai gobarar ta shafa.”

Mai magana da yawun Hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya, Ibrahim Mohammad, ya tabbatarwa da majiyar da faruwar lamarin, amma ya ce ƙarama ce.

Ya ce, an shawo kan lamarin kuma an dawo da zaman lafiya.

Ita ma da take mayar da martani, kakakin rundunar ’yan sandan Birnin Tarayya, Josephine Adeh ta ce an tura jami’an ’yan sanda wurin da lamarin ya faru domin kare yankin da kuma hana sace-sacen jama’a.

“Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:40 na asubahi, nan take muka tura mutanenmu wurin domin su tsare wurin da kuma hana duk wani abu da ya saɓa wa zaman lafiya,” in ji ta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
  • Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja
  • Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar
  • Tinubu ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu manyan laifuka
  • AA Zaura Ya Yi Kira Ga ’Yan Nijeriya Su Marawa Sauye-sauyen Shugaba Tinubu Baya
  • Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba
  • Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba
  • Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru
  • Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a Kaduna