Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka
Published: 6th, July 2025 GMT
Elon Musk, wanda ya taɓa zama mashawarcin Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna America Party.
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter), makonni bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsa da Shugaban Amurka.
Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–KanoMusk, wanda attajirin mai kuɗi sosai, ya ce jam’iyyarsa za ta kasance wata hanya ta daban daga jam’iyyu biyu da ake da su yanzu, wato Republican da Democrat.
Amma har yanzu ba a bayyana ko hukumar zaɓen Amurka ta amince da rajistar jam’iyyar ba.
Amma Musk bai bayyana wanda zai jagoranci jam’iyyar ko irin manufofinta ba.
Tun da farko Musk ya fara maganar kafa sabuwar jam’iyya ne bayan samun saɓani da Donald Trump, wanda hakan ya kai sa ga sauka daga matsayinsa a gwamnatin Trump.
Yayin wata ƙuri’ar jin ra’ayi da ya gudanar a X, mutane miliyan ɗaya ne suka kaɗa ƙuri’a, kuma kashi 60 daga cikinsu sun amince a kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sabuwar Jam iyya Saɓani Zaɓe kafa sabuwar jam
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp