UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
Published: 10th, July 2025 GMT
A gabanin bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD, taron kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD wato UNHRC karo na 59 ya zartas da kudurin da kasar Sin ta gabatar dangane da muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam. Wannan ne karo na farko da aka zartas da kudurin ta hanyar tattaunawa a maimakon kada kuri’a.
Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da kungiyoyin kasa da kasa a kasar Switzerland ya yi karin bayani kan kudurin da cewa, kudurin ya sake nanata muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam daga dukkan fannoni, tare da jaddada yadda ci gaba mai inganci kuma mai mayar da jama’a a gaban kome, yake taka muhimmiyar rawa kan kyautata jin dadin jama’a da kuma kara azama kan bunkasar hakkin dan Adam.
Har ila yau, kudurin da kasashe 42 ciki har da Kamaru da Pakistan suka gabatar cikin hadin gwiwa ya bayyana fatan kasashe masu tasowa. Wakilai daga kasashen Cuba, Bolivia, Habasha, Kenya sun bayyana cewa, kudurin zai kyautata kulawar da ake nunawa kan muhimmancin ci gaba wajen kiyaye hakkin dan Adam da kuma kara azama kan kiyaye hakkin dan Adam ta hanyar samun bunkasa mai dorewa. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kiyaye hakkin dan Adam
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Ta Kashe Falasdianwa 6 A Gaza, Kuma Tsoffin Fursinoni
Wani babban jami’I a kungiyar Hamas ya bayyana cewa sojojin HKI sun kashe falasdinawa guda 6 a zirin gaza a ci gaba kissan kiyashin da takewa falasdinawa a yankin.
Abdul-Karim Hanini, ya kara da cewa wadanda ta kashen tsoffin fursinoni a hannun yahudawan a shekarun da suka gaba 5 daga cikinsu an yi musayarsu ne a shekara 2011 a lokacinda aka yi musayarsu da fursinan yahudawan Galid Shalit a shekarar. Sannan dayan kuma an yi musayarsa ne a shekara ta 2002 wanda yahudawan suka kora daga Cocin Nativity daga birnin Bethlaham a yankin yamma da kogin Jordan.
Abdul-Karim Hanini ya kammala da cewa a dai dai lokacinda muke makokin yan’uwammu da yahudawan suka kai ga shahata, muna rokon All..ya karbi shahadarsu, sannan muna kara nanata cewa zamu ci gaba da gwagwarmaya da su har zuwa jinni na karshe da zamu iya zubarwa ko kuma mu sami nasara a kansu.