Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a
Published: 29th, October 2025 GMT
Asalin tsarin shari’ar da ake amfani da shi game da kare muradun al’umma ya bai wa masu gabatar da kara damar yin aiki na neman hukunta masu laifi a madadin sauran al’umma a shari’o’in da suka shafi laifukan gurbata muhalli, da rashin kiyaye tsaftar abinci, da kuma rashin da’a ga gwamnati wadanda dukkansu idan aka bar su kara-zube, za su tauye hakkokin galibin jama’a.
Domin ganin ba a tauye hakkin kowane bangare tsakanin mahukunta da mabiya ba, a karkashin daftarin dokar, dole ne masu gabatar da kara su fara gabatar da bukatar hukumomin gwamnati da su sauke nauyin da ke wuyansu kafin shigar da kara a kansu. A bangaren kare hakkin jama’a kuma, an haramta daukar matakan tilastawa kamar hana mutum amfani da asusunsa na banki da kadarori ko takaita ‘yancin walwala a yayin gudanar da bincike. Kazalika, an karfafa gwiwar ‘yan kasa da kungiyoyin kyautata zamantakewa su bayar da rahoton keta hakkokin jama’a da kuma sa ido kan shari’o’in da ake gudanarwa kan hakan.
Daga shekarar 2015 zuwa 2025, hukumomin da ke kula da share hawayen jama’a a bangaren shari’a sun yi aiki a kan korafe-korafe fiye da miliyan 1.22 wadanda galibi aka gabatar a kan ma’aikatun gwamnati.
Su dai tsare-tsaren da ake amfani da su na kare muradun jama’a a kasar Sin ba a tattare suke a wuri guda ba, suna warwartse ne a karkashin dokokin gudanarwa na fararen hula daban-daban, amma wannan daftari ya hade su wuri guda.
Kokarin tabbatar da wannan daftarin doka na kare muradun al’umma a kasar Sin, babu shakka ya kara fito da burin kasar na gyare-gyare a dukkan fannoni tare da cike gibin da ake ganowa, yayin da kasar ta hau turbar cimma burin zamanintarwa a karkashin tsarin gurguzu nan da shekarar 2035. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika
Idan muka kwatanta da kasar Sin, sabanin yawan albarkatun da Afrika ke da su kamar na kasar noma, ita Sin kasa da kaso 9 kadai take da shi, amma kuma tana bayar da gagagrumar gudunmawa a duniya, inda take tsaye da kafarta wajen ciyar da al’ummarta, har ma ta bayar da gudunmawa ga kasashe mabukata.
To mene ne dalilin nasarar Sin a wannan bangare?
Gaggarumar nasarar da Sin ta samu a bangaren aikin gona, ba wani abu ba ne illa jajircewar gwamnatin kasar da dabaru da fasahohin aikin gona da kullum ake lalubowa. Misali, ko a cikin hamada, kasar Sin ta lalubo dabarun da suka dace, inda ake noman tsirrai masu juriya dake iya ciyar da mutane da samar da kudin shiga tare da yaki da kwararar hamada. Haka kuma, fasahohinta na samar da ingantattun iri da noma cikin daki ko rumfa, duk abubuwa ne da suka bunkasa yabanya a kasar. Ga uwa uba kayayyakin aiki na zamani da manomanta ke amfani da su. Za mu iya bayyana aikin gona a kasar Sin a matsayin wata sana’a ta zamani sabanin yadda ake ganinta a matsayin sana’a mai wahala da bata samar da kudin shiga.
La’akari da yawan jama’a da yadda ta kasance koma baya, tabbas nahiyar Afrika na bukatar fasahohin Sin domin fitar da al’ummominta daga kangin talauci tare da wadatar da su da abinci. Dabaru da fasahohin Sin, za su yi wa bangaren aikin gona a nahiyar gagarumin garambawul, domin idan aka tabbatar da hada fasahohin da tarin albarkatun da nahiyar take da su, to kasashen Afrika za su iya tsayawa da kafarsu, su kuma fatattaki yunwa da talauci, da karfafa gwiwar matasa ta yadda za su rika ganin aikin gona a matsayin wata sana’a mai riba. Tabbas ingantattun fasahohin aikin gona na Sin, za su taka rawar gani wajen kyautata makomar nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA