An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa
Published: 24th, July 2025 GMT
Kwamitin zartaswa na Jam’iyyar APC na ƙasa ya naɗa Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa.
Nan take aka rantsar da Nentawe Yilwatda a wajen taron.
Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a ChinaNentawe ya yi rantsuwar ne da misalin ƙarfe 02:50 na rana a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar yayin taron NEC karo na 14 da ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, ranar Alhamis.
Nentawe, wanda ya fito daga Jihar Filato, shiyyar Arewa ta Tsakiya, shi ne ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Abdullahi Umar Ganduje Nentawe Yilwatda
এছাড়াও পড়ুন:
Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
Da yammacin yau Alhamis ne firaministan kasar Sin Li Qiang, ya shugabanci taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da EU karo na 25, tare da shugaban majalisar EU Antonio Costa, da shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen a nan birnin Beijing.
A yayin taron, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da EU suna da moriya iri daya wadda babu rikici a cikinta. Bisa yanayin sauyi da ake ciki a halin yanzu, ya kamata Sin da EU su kara yin hadin gwiwa. Kuma kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da bangaren EU a fannonin cinikayya, da zuba jari, da kiyaye muhalli, da kimiyya da fasaha da sauransu, don tabbatar da samar da kayayyaki a tsakaninsu yadda ya kamata, da kiyaye yin shawarwari da juna, domin daidaita matsalolin dake tsakaninsu, ta yadda za a kara samun nasarori a hadin gwiwarsu.
Li Qiang ya ce, kamata ya yi bangarorin biyu su kara yin hadin gwiwa, da tabbatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da gudanar da ciniki cikin ‘yanci, don tabbatar da adalci da odar tattalin arziki, da cinikayya a duniya baki daya.
A nasu bangare, Antonio Costa da Ursula von der Leyen, sun bayyana cewa, bangaren EU yana fatan yin kokari wajen zurfafa dangantakar abokantaka a tsakaninsa da kasar Sin a dogon lokaci, da kara yaukaka mu’amala da juna, da fahimtar juna, da mai da hankali ga batutuwan da suke mayar da hankali a kansu, da sa kaimi ga hadin gwiwarsu a fannonin cinikayya da zuba jari, da kokari tare wajen tinkarar kalubalen duniya, da nuna goyon baya ga hukumar WTO, ta yadda za ta taka muhimmiyar rawar raya dangantakar tattalin arziki, da cinikayya a tsakanin sassan kasa da kasa, da kuma tabbatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp