Aminiya:
2025-11-02@00:52:57 GMT

Haɗakar ’yan hamayya alheri ce ga siyasar Nijeriya — Gbajabiamila

Published: 13th, July 2025 GMT

Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila ya ce haɗakar ’yan siyasa a jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Nijeriya.

Ya bayyana cewar haɗaka ’yan adawar za ta taimaka wajen hana ƙasar faɗawa cikin siyasar jam’iyyar ƙwaya ɗaya tal.

WFP ya dakatar da tallafin abinci a Yammaci da Tsakiyar Afirka Za a sa zare tsakanin Amurka da Turai kan harajin kasuwanci

Gbajabiamila ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a Jihar Legas a jiya Asabar a mazaɓarsa da ke Surulere.

Sai dai tsohon shugaban Majalisar Wakilan ya bayyana shakkunsa kan haɗakar, inda ya ce ce ba ya tunanin za ta yi wani tasirin a-zo-a-gani.

“Muna maraba da samar da haɗakar. Ai ba wannan ba ne karo na farko da aka samu haɗakar ’yan siyasar a wannan ƙasar tamu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “a dimokuraɗiyya ana buƙatar hamayya mai ƙarfi, domin idan babu hamayya mai ƙarfi, za mu iya faɗawa siyasar jam’iyyar ɗaya,” in ji shi.

A bayan nan ne dai wasu fitatun ’yan jam’iyyun hamayya ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da sauransu suka ayyana jam’iyyar haɗaka ta ADC domin fuskantar Zaɓen 2027, inda suke fatan za su kayar da Bola Tinubu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: adawa Haɗaka Hamayya

এছাড়াও পড়ুন:

PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike

Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne.

Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u

Sauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka dakatar ba sa halartar tarukan jam’iyyar.

An dakatar da su na tsawon wata ɗaya, sannan aka miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar PDP domin gudanar da bincike.

Waɗanda aka dakatar ’yan tsagin Wike ne, kuma sun raba ƙafa a rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaɓen 2023.

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne, wata Babbar Kotu a Babban Birnin Tarayya, ta dakatar da PDP daga shirin gudanar da babban taronta da aka tsara yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.

Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron ba.

Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun ce rashin jituwa a PDO shi ne babban dalilin da ya sa aka kai ƙarar taron’ kotu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum
  • Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar
  • PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?
  • Babban Daraktan Sakatariyar APEC: Sin Tana Ba Da Gudummawar Ba Da Jagoranci A APEC
  • Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba