Sin Za Ta Harba Kumbon Shenzhou-21
Published: 30th, October 2025 GMT
Hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati ta kasar Sin ko CMSA, ta ce an shirya harba kumbon Shenzhou-21 da karfe 12 saura mintuna 16 na daren gobe Juma’a, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Yayin taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis, CMSA ta sanar da cewa, ‘yan sama jannati Zhang Lu, da Wu Fei da Zhang Hongzhang, za su kasance cikin kumbon na Shenzhou-21, kuma Zhang Lu ne zai jagoranci tawagar.
A cewar kakakin CMSA Zhang Jingbo, Sin na rike da kudurinta na sauka kan duniyar wata kafin shekarar 2030, ta kuma tsara jadawalin samar da ci gaba, da gwajin babban aikinta na sauke ‘yan sama jannatinta kan doron wata.
A wani ci gaban, CMSA ta ce ‘yan sama jannati biyu na kasar Pakistan za su samu horo tare da takwarorinsu na Sin, kuma za a zabi daya daga cikinsu don kasancewa tare da kumbon Sin na dakon ‘yan sama jannati na dan wani lokaci a matsayin kwararren jami’i. (Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: yan sama jannati
এছাড়াও পড়ুন:
Al-Burhan: Sojojin Sudan Sun Janye Daga El-Fasher Saboda Kare rayukan Fararen Hula
Babban hafsan hafsoshin Sojin Sudan kuma shugaban majalisar gudanar da mulkin kasar ya bayyana cewa; Rundunar sojin kasar ta bar birnin El Fasher ne domin gujewa “kisan fararen hula” da dakarun kai daukin gaggawa ke yi
Shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin Soja ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce: shugabannin sojoji sun yanke shawarar barin birnin El Fasher da ke Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan ne, domin kare birnin da ‘yan kasar daga afkawa cikin matsalar kisan kai a hannun Rundunar Rapid Support Forces ta dakarun Kai Daukin Gaggawa.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu, al-Burhan, wanda ke jagorantar rundunar sojin Sudan, ya ce a wani jawabi da aka watsa ta talabijin a gidan talabijin na gwamnati: “Kowa yana bin abin da ya faru a El Fasher, kuma shugabannin da ke can, ciki har da kwamitin tsaro, sun yanke shawarar cewa dole ne su bar birnin saboda halaka da kisan fararen hula.”
Ya bayyana cewa shugabannin sojoji a El Fasher “sun yanke shawarar barin birnin, kuma sun amince da fice daga cikinsa, bisa sharadin cewa za su bar birnin zuwa wuri mai aminci don ceton sauran ‘yan kasar da sauran birnin daga halaka.” Ya kara da cewa: “Wannan yana daya daga cikin matakan ayyukan soji da aka dora musu a matsayinsu na al’ummar Sudan, kuma koyaushe suna fadin hakan, kuma suna maimaitawa: al’ummar Sudan za su yi nasara, kuma Sojojin Sudan za su yi nasara.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Baqaei: Iran ta daɗe tana aiki don haɓaka zaman lafiya a duniya October 28, 2025 An Yi Girgizar Kasa Mai Karfi A Kasar Turkiya October 28, 2025 Ouattara Na Kasar Ivory Coast Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa October 28, 2025 MDD Ta Yi Kira Da Abude Kafar Shigar Da Kayan Agaji Zuwa Garin El-Fashar October 28, 2025 Wilayati: Kasashen Ian, China Da Rasha Suna Taka Rawa A Fagen Kafa Sabon Tsarin Duniya October 28, 2025 Zaben Ivory Coast: Alassane Ouattara na kan gaba da tazara mai yawa October 27, 2025 Pezeshkian: Hadin kan Musulmi zai iya dakile zalincin kasashen waje October 27, 2025 Amurka ta tsare wani dan jarida musulmi saboda sukar Isra’ila October 27, 2025 Kashi 84% na ‘yan Faransa ba su gamsu da Macron ba a matsayin Shugaba October 27, 2025 Iran ta bukaci MDD ta nisanci nuna bangaranci game da masu keta dokokin duniya October 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci