Aminiya:
2025-12-15@08:06:48 GMT

Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata

Published: 30th, October 2025 GMT

A ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin Nahiyyar Afirka na 2026 da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci, yanzu haka ƙasashe 6 sun samu nasarar shiga gasar.

Ƙasashen da suka samu tikitin sun haɗa da mai masaukin baƙi: Morocco  da Najeriya da Zambia da Tanzania da Malawi da Algeria da Ghana da Senegal da Kenya da Burkina Faso da Cape Verde da Afrika ta Kudu.

Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29 ACF ta mara wa gwamnatin Tinubu baya

Wannan dai ita ce gasa karo na 14 da za a buga a tarihi daga ranar 17 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu na 2026.

Ƙasashen da suka kai wasan kusa da na ƙarshe a Kofin Nahiyyar Afirkan za su wakilci nahiyar a Kofin duniya na mata da za a buga a ƙasar Brazil a 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kenya kofin Nahiyyar Afirka na 2026 Malawi

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda aka yi bikin naɗa Rarara sarkin wakar ƙasar Hausa a Daura

Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Faruk Umar Faruk, ya naɗa fitaccen mawaƙin siyasar nan na Hausa, Dauda Kahutu Rarara, a matsayin Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa.

An yi bikin naɗin sarautar ne a garin Daura a ranar Asabar 13 ga watan Disamba, 2025 domin karrama rawar da Rarara yake takawa wajen haɓaka waƙoƙin Hausa da kuma tasirin da yake da shi a fagen nishaɗi da al’adu.

Jirgin sama ya yi hatsari yayin sauka a Kano Tsaro: Abba ya kafa runduna ta musamman da za ta ke tsaron tashoshin mota a Kano

Tun da farko mawaƙin da kansa ya wallafa goron gayyatar naɗin sauratar da za a yi masa a shafinsa na Facebook, a ranar 9 ga watan Disamba, 2025.

Rarara ya ce: “Ina gayyatar kowa da kowa zuwa wajen naɗin sarautata, mai taken ‘Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa’ sarautar da mai Alfarma Sarkin Daura ya yi min.

“Za a yi naɗin a fadar Mai Martaba Sarkin Daura a ranar Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025, insha’Allah Allah.”

Bikin naɗin sarautar ya samu halartar manyan mutane, mawaƙa, jarumai, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibirin, Ali Nuhu da sauransu, inda masoya da magoya bayan mawaƙin suka nuna farin cikinsu.

Masoyan mawaƙin sun bayyana cewa wannan karramawa ta dace da gudunmawar da Rarara ya bayar ga al’adun Hausawa.

Rarara, wanda ya shahara wajen yin waƙoƙin siyasa da na zamantakewa, ya daɗe ana damawa da shi kuma yana daga cikin manyan mawaƙa a Arewacin Najeriya.

Sabuwar sarautar da aka yi masa na nuni da amincewa da gudunmawarsa wajen bunƙasa waƙa a harshen Hausa da kuma tasirinsa a cikin al’umma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ECOWAS ta jaddada aniyar kare dimokuraɗiyya da inganta tsaro a yammacin Afirka
  • Yadda aka yi bikin naɗa Rarara sarkin wakar ƙasar Hausa a Daura
  • Eritrea Ta Fice Daga Kungiyar Raya Kasahsen Gabacin Afrika (IGAD)
  • An kashe mai ciki da ɗanta a Kano
  • NEPC Ta Horas da Mata Kan Damar Kasuwancin Fitar da Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje
  • Wacce Kasa Ce Za Ta Lashe Gasar Kofin Afirka
  • Yadda za ku cike neman aikin jami’an lafiya a Hajjin 2026 da NAHCON
  • Yadda za ku nemi aikin jami’an lafiya a Hajjin 2026 da NAHCON
  • Zan yi amfani da Salah a wasan Liverpool da Brighton — Arn Slot
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji