DSP Abdullahi ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike, tare da roƙon mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu kuma su taimaka wa ‘yansanda da bayanai.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra October 29, 2025 Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Duk da ce-ce-ku-ce sunan Maryam Sanda na cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa

Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa wasu wadanda suka hada da masu manyan laifuka kamar kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu.

A baya dai wasu sun yi ta suka da ce-ce-ku-ce kan sanya sunan Maryam Sanda cikin wadanda shugaba Tinubu ya yi wa afuwa.

Tinubu ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu manyan laifuka Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin Afrika

Duk da maganganun mutane sunan Maryam Sanda na cikin sabon jerin sunayen wadanda aka bari, bayan cire wasu.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunan aƙalla mutum 50 daga tsohon jerin sunayen da aka fitar bayan ce-ce-ku-cen jama’a.

“Bayan martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen waɗanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, da fataucin mutane daga jerin waɗanda aka yi wa afuwa,” in ji Onanuga.

Ya ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne “don mutunta ra’ayoyin jama’a, inganta haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa da al’umma baki ɗaya.”

Tsohon jerin sunayen da aka fitar ya haifar da cece-kuce a tsakanin jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.

Sun bayyana matakin a matsayin amfani da ikon shugaban ƙasa ta hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan barazana ce ga tsarin shari’a.

Sun yi gargaɗin cewa sakin waɗanda suka aikata manyan laifuka zai iya ƙarfafa aikata laifi da kuma rage wa doka tasiri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Duk da ce-ce-ku-ce sunan Maryam Sanda na cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra
  • Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC
  • Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Abinci Ba – ADC
  • ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa
  • Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajali Tare Da Jikkata Wasu A Gombe
  • An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi
  • Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe
  • Saukar Farashin abinci: Manoma da gwamnati na nuna wa juna yatsa