Kamfanin Amazon na shirin sallamar ma’aikata 600,000 don maye gurbinsu da mutum-mutumi
Published: 30th, October 2025 GMT
Kamfanin Amazon, wanda shi ne na biyu a yawan ma’aikata a Amurka, zai sallami ma’aikata kusan 600,000 ta hanyar maye gurbin su da mutum-mutumi nan shekaru 10 masu zuwa.
Wani rahoton takardun cikin gida na kamfanin ne ta bayyana hakan, kamar yadda jaridar The New York Times ta Amurka ta wallafa.
Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29 Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35
A cewar rahoton, wannan dabarar na fitowa ne daga masu lura da ma’aikata na kamfanin da alkaluman su ke nuna cewa kamfanin na iya kauce wa ɗaukar fiye da mutum 160,000 da ake bukata a Amurka nan da shekarar 2027.
Kamfanin dillancin kaya na Amazon ya taɓa bayyana cewa amfani da mutum-mutumi zai ba shi damar faɗaɗa kasuwancinsa zuwa ninki biyu na yawan kayayyakin da yake siyarwa nan da shekarar 2033, ba tare da ƙara yawan ma’aikata a Amurka ba.
Tarin takardun da aka tattara tare da hirarraki da jaridar ta gudanar ya nuna cewa wannan sauyi zai sa kamfanin ya zama ba ya buƙatar ɗaukar fiye da mutum 600,000 a cikin shekaru goma masu zuwa.
Sai dai Amazon ya ƙi amincewa da sakamakon binciken na jaridar.
A cikin wata wasika da ta aike wa The Independent, Amazon ya ce adadin mutum 600,000 ya fito ne daga wata takarda daga sashe guda na kamfanin, wanda ba shi da alaka da ɗaukar ma’aikata.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata zargin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka yi cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Ministan Watsa Labarai, Mohammed Idris, ya ce wannan zargi ya ta’allaƙa ne da bayanai marasa tushe, waɗanda ba su san yanayin tsaron Najeriya ba.
“Wasu daga cikin iƙirarin da jami’an Amurka suka yi sun dogara ne da bayanai marasa inganci da tunanin cewa yawancin waɗanda ake kai wa hare-hare Kiristoci ne,” in ji Idris.
“Waɗannan miyagu (’yan ta’adda) ba su ware addini ɗaya ba, suna kai wa Kiristoci da Musulmai hari musamman a Arewacin ƙasar nan.”
Ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai yawan addinai da ke zaune lafiya tare, kuma irin waɗannan rahotanni na ƙarya na iya haddasa rikici da tayar da fitina.
“Keɓe waɗannan hare-hare da sunan wani addini abu ne mai hatsarin gaske. Najeriya ƙasa ce wadda mutane suka yadda da juna inda mutane masu addinai daban-daban ke rayuwa cikin lumana,” in ji ministan.
Idris, ya ce gwamnati na ci gaba da inganta fannin tsaro, ciki har da samar da sabbin kayan aiki da haɗin kai mai ƙarfi tsakanin hukumomin tsaro.
Ya bayyana cewa tun daga shekarar 2009, Najeriya ke yaƙi da ta’addanci da ’yan fashin daji, kuma sauye-sauyen da aka yi kwanan nan sauke Hafsoshin Tsaro na nufin inganta tsaro.
Ministan, ya ƙara da cewa gwamnati tana amfani da hanyoyin zaman lafiya ta hanyar noman abinci, samar da ayyukan yi, da shirye-shiryen tallafa wa jama’a don rage talauci da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma.