DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya
Published: 29th, October 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin manyan jam’iyyar a matakin kasa sun nuna adawa da niyyar Lamido na neman kujerar shugabancin PDP, suna ganin cewa ba shi ne ya dace da wannan matsayi a yanzu ba.
Wannan lamari ya sake haska yadda PDP ke ci gaba da fama da rikicin cikin gida, wanda da yawa ke ganin zai iya shafar karfinta da hadinta kafin babban zaben da ke tafe.
Wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kabiru Tanimu Turaki
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Sha Alwashin Wadata Al’ummarsa da Tsaftataccen Ruwan Sha
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba, ya umarci a gaggawata gyaran bututun da suka hada tashar tacewa da samar da ruwa yankunan Dutsawa da Kantudu.
Wannan mataki ya biyo bayan matsalolin da ake yawan fuskanta sakamakon lalacewar wutar lantarki da na’urar janareto, wanda ke hana jama’a samun ruwa yadda ya kamata.
Yayin da yake bayyana jimaminsa bisa wannan lamari, Dr. Muhammad Uba ya basu tabbacin cewa In Shaa Allahu matsalar ta zo karshe.
A cewarsa, majalisar ta kudirin aniyar yin duk mai yiwuwa domin magance matsalolin da ake fuskanta tare da tabbatar da samun isasshen tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.
Ya yi alkawarin tura dukkan kayan aiki da ake bukata domin ganin an warware matsalar.
Dr. Muhammad Uba ya kuma bukaci ma’aikatan hukumar ruwa ta Birnin Kudu da su kara jajircewa wajen kula da tsarin domin kauce wa sake fuskantar irin wannan matsala a gaba.
“Ina karfafa gwiwar dukkan ma’aikatan hukumar ruwa da su kasance masu lura, su zama masu saurin daukar mataki, kuma su kawar da duk wani cikas da zai hana cimma burin samar da ruwa mai dorewa a ko’ina cikin Birnin Kudu.”
Shugaban ya bayyana cewa aikin da ake yi a babbar tashar tacewa da samar da ruwan sha ya kusa kammaluwa.
A cewarsa, wannan aikin tare da gyaran bututun da ake yi yanzu na daga cikin babban shirin gwamnatinsa na inganta samar da ruwa a fadin karamar hukumar.
Wasu daga cikin mutanen yankin sun ce wannan mataki ya nuna jajircewar Dr. Uba wajen inganta muhimman ababen more rayuwa da kuma kyautata jin dadin al’ummar Birnin Kudu.