Aminiya:
2025-12-13@19:26:16 GMT

Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sanusi

Published: 29th, October 2025 GMT

Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammadu Sanusi II, ya bai dace gwamnatin Shugaban Kasa Bola tinubu ta ci gaba da ciyo bashi ba bayan ta cire tallafin man fetur.

Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Talata, a taron Oxford Global Think Tank Leadership da ƙaddamar da wani littafi, Sanusi ya ce cire tallafin man ya haifar da ƙaruwar kuɗaɗen shiga na gwamnati.

Netanyahu ya ba da umarnin kai mummunan farmaki a Gaza Amurka ta soke bizar Wole Soyinka

Sanusi ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗi, yana mai bayyana matakan a matsayin “masu raɗaɗi amma na wajibi.”

Sai dai ya yi gargaɗin cewa waɗannan gyare-gyare ba za su yi tasiri ba sai an haɗa su da tsari mai kyau na kashe kuɗi da gaskiya a cikin gudanar da gwamnati.

“In ka daina biyan tallafi amma ka ci gaba da yin rance, hakan na nufin ka rufe rami guda ne sai ka buɗe wani. Kalubalen da ke gabanmu yanzu shi ne ingancin yadda gwamnati ke kashe kuɗi da kuma yadda ake tafiyar da kuɗaɗen da aka ce an ajiye,” in ji shi.

Sanusi, wanda ya jagoranci CBN daga 2009 zuwa 2014, ya ce matsalolin tattalin arzikin Najeriya a yanzu sun faru ne a sakamakon rashin daidaito a manufofi da siyasar neman sai an faranta wa jama’a da aka dade ana yi.

“A shekarar 2012, mun yi gargaɗin cewa tallafin mai ba zai dore ba, amma siyasa ta shigo. Yanzu, waɗanda suka jagoranci zanga-zangar adawa da cire tallafin su ne suka gaji matsalar, kuma ba su da wani zaɓi sai su yi abin da ya dace,” in ji shi.

Ya yaba wa ƙwararrun da ke cikin tawagar tattalin arzikin gwamnati kan matakan da suka ɗauka don daidaita hauhawar farashi da rage canjin farashin kuɗi, amma ya jaddada cewa dole ne a dakile ɓarna da almubazzaranci cikin gaggawa.

Yayin da yake tambaya kan yadda gwamnati ke kashe kuɗi, Sanusi ya ce: “Me ya sa muke da ministoci 48? Me ya sa ake da jerin motocin gwamnati masu yawa? Me ya sa har yanzu ana yin rance bayan cire tallafi? In ka rufe rami guda, me ya sa za ka buɗe wani?

“Wannan gwamnati na bukatar ta duba hukumomi da yadda ake amfani da kuɗi a dukkan matakai. Domin in ka ci gaba da samun kuɗi amma kana kashewa ba daidai ba, za ka lalata duk wani ci gaba da aka samu.

“Amma irin mu da za mu ce, ‘Ya Shugaban Ƙasa, wannan ba daidai ba ne,’ ana ɗaukarmu a matsayin abokan gaba. Don haka, idan shugabanni sun kewaye kansu da masu yabon kai, ba za su taɓa samun shawara mai kyau ba.

“Shi ya sa irin su Aigboje Aig-Imoukhuede da ni kan zama kamar abokan gaba ga gwamnati, domin mutane ba sa son jin gaskiya.”

Sanusi ya ƙara da cewa: “Mun faɗa wa Buhari komai, game da buga kuɗi, almubazzaranci, farashin musayar kuɗi da tallafi, amma duk lokacin da muka yi hakan, ana ɗauka a matsayin hari kai tsaye. Waɗanda ke kewaye da shi sun sa ya ɗauke mu a matsayin abokan gaba. Shugabanni dole su fara tambaya: wa nake kewaye da kaina da su?,” in ji Sanusi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: cire rallafin mai

এছাড়াও পড়ুন:

Mangal ya bayar da tallafin N257m don yi wa marasa galihu aikin ido kyauta a Katsina

Fitaccen attajirin nan Alhaji Dahiru Mangal, ya ɗauki nauyin yi wa marasa galihu a Jihar Katsina aikin ido kyauta, inda ɗaruruwan mutane ke samun kulawar likitoci ba tare da biyan ko sisi ba.

A yayin da wakilin Aminiya, ya ziyarci Asibitin Ido da ke birnin Katsina, marasa lafiya da dama da suka ci gajiyar aikin sun bayyana farin cikinsu da godiya kan tallafin na sama da Naira miliyan 257.

Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699 Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda

Malama Indo, wadda ta fito daga garin Dankama da ke Ƙaramar Hukumar Kaita, ta bayyana farin cikinta da samun tallafin.

Ta ce: “Na kwashe kusan shekara guda ina fama da ciwon ido. Da zarar yamma ta fara yi, sai na kasa fitowa saboda duhu. Amma yanzu ina gani lafiya lau, babu wata matsala.

“Mun kwana uku a nan asibiti, ba mu rasa komai ba, har abinci ake ba mu. Wallahi ba zan iya cewa na kashe komai ba sai kuɗin mota kawai.

“Muna roƙon Allah Ya saka wa wanda ya ɗauki nauyin wannan aiki da alheri,” in ji ta.

Shi ma wani dattijo mai suna Malam Khalha Jibiya, ya bayyana jin daɗinsa game da aikin.

Ya ce an masa aiki, an kuma ba shi tabarau, sannan yanzu yana gani ba tare da wata matsala ba.

“Idan waɗanda Allah Ya hore musu dukiya za su riƙa taimaka wa gajiyayyu kamar haka, da matsalolinmu da dama sun ragu.

“Muna addu’a Allah Ya saka wa mai ɗaukar nauyin wannan shiri da alheri.” inji Malam Khalha.

Dukkanin marasa lafiyan da Aminiya ta zanta da su, sun yi godiya, musamman ganin cewa aikin ido da magungunan da ake ba su kyauta ne baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Samarwa Sojoji Manyan Makamai Ne Mafita – Shugaban Ƙaramar Hukumar Bukuyum
  • Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago
  • Mangal ya bayar da tallafin N257m don yi wa marasa galihu aikin ido kyauta a Katsina
  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda
  • Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba
  • ‘Yan Siyasa Ne Ke Zagon Ƙasa Ga Ci Gaban Nijeriya — Sarki Sanusi II
  • ‘Sojojin Najeriya da na Ivory Coast 200 sun shiga domin tsaftace Jamhuriyar Benin’
  • BUA ya tallafa wa ɗaliban Sakkwato 200 da miliyan 40
  • Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC