Aminiya:
2025-11-02@19:57:06 GMT

’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja

Published: 10th, July 2025 GMT

Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, ciki har da ɗan sanda da ’yan sa-kai guda uku, a wani hari da ’yan bindiga suka kai garin Mongoro da ke Ƙaramar Hukumar Mariga, a Jihar Neja.

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Laraba.

Ana zargin takalar faɗa tsakanin fadar Aminu Ado da Sanusi II ’Yan ƙabilar Ibo ne suka fi aikata laifi a Jihar Anambra ba Fulani ba — Gwamna Soludo

Mazauna garin Wamba, sun ce har yanzu suna cikin fargaba saboda ‘yan bindigar ba su bar yankin ba.

A ranar 24 ga watan Yuni, maharan sun kai hari wani sansanin sojoji da ke Kwanan-Dutse, inda suka kashe sojoji 17, tare da jikkata wasu 10.

A cewar wasu mazauna garuruwan, harin na baya-bayan nan ya faru ne a ranar Talata, inda ’yan bindigar suka zo da yawa kuma ɗauke da muggan makamai inda suka yi wa jami’an tsaro da ’yan sa-kai taron dangi.

Sun raunata mutane da dama.

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce jami’an tsaron sun yi ƙoƙari, amma alburusansu sun ƙare a yayin artabun, wanda hakan ya sa dole suka ja da baya.

Ya ce ana buƙatar gaggauta tallafa wa ’yan sa-kai a Mongoro saboda yankin na fama da hare-hare.

Wani mazaunin kuma ya ce an kashe mutum 13, ciki har da ’yan sa-kai, sannan ’yan bindigar sun lalata turakun sadarwa, wanda hakan ya haddasa matsalar sadarwa a yankin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya tabbatar da harin, amma ya ce ba a tabbatar da adadin waɗanda suka rasu ba tukuna.

Ya ƙara da cewa lamarin tsaro a yankin na ƙara taɓarɓarewa saboda yawan hare-haren da ake kai wa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce har yanzu babu cikakken bayani.

Saboda tsoron kai hare-haren, manoma da dama a Mariga da Rijau sun daina zuwa gonaki, wasu kuma sun koma birane domin tsira da rayukansu.

Wani mazaunin yankin Rijau, mai suna Ibrahim Ayuba, ya ce mutane da yawa sun tsere daga ƙauyuka zuwa Rijau saboda tsoron kashe-kashe da sace-sacen da ke ƙaruwa a kullum.

A wani yunƙuri na shawo kan matsalar tsaro, Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, ya buƙaci haɗin gwiwa da sabbin dabaru domin magance matsalar.

Ya bayyana haka ne yayin da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Adamu Abdullahi Elleman, ya kai masa ziyara a fadarsa.

Kwamishinan, ya ce manufar ziyarar ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin sarakuna, al’umma da jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro.

Masani ya buƙaci kafa rundunar tsaron daji

Wani masani kan harkar tsaro, Auwal Bala Durumin Iya, ya buƙaci gwamnati ta bai wa ’yan sa-kai da jami’an tsaro makaman da suka fi ‘yan bindiga nagarta.

Ya kuma bayar da shawarar a kafa sabuwar rundunar tsaro domin kula da dazuka, wanda yawancin a can ake aikata laifuka.

Ya ce dole ne a horas da dakarun rundunar sosai, a ba su makamai irin su AK-47, sannan a cire siyasa wajen kula da harkar tsaro.

Ya ce idan aka daina siyasantar da harkar tsaro, aka mayar da hankali kan ƙwarewa, za a iya cimma nasara.

Ya kuma buƙaci gwamnati ta naɗa shugabanni nagari a hukumomin tsaro, tare da tallafa wa ’yan sa-kai da kuɗi da kayan aiki, inda ya yaba wa ƙoƙarinsu duk da cewa ba sa karɓar albashi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan sa Kai hari Jami an Tsaro Ƙauyuka Mariga Tsaro jami an tsaro yan bindiga Yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’

Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.

Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka.

Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare.

Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar.

 

BBC

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure