Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
Published: 30th, October 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya nemi sabbin hafsoshin tsaron ƙasar su zage damtse domin magance duk wata barazanar tsaro da ake fuskanta a halin yanzu da ma wadda ka iya kunnowa nan gaba.
Shugaban ya gargadi sabbin hafsoshin tsaron cewa ’yan Nijeriya sakamako kawai suke buƙata, ba uzuri ba, saboda haka dole ne su cika aikin da aka ɗora musu.
Tinubu ya bayyana hakan ne bayan bikin ƙara wa sabbin hafsoshin tsaron da shugabannin rundunonin soji girma da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa yau Alhamis a Abuja.
A cewarsa, “Barazanar tsaro na ƙara sauyawa a kodayaushe, kuma abin da ya fi damun gwamnatinmu shi ne ɓullar sababbin ƙungiyoyin ’yan bindiga a Arewa ta Tsakiya, da Arewa maso Yamma, da wasu sassa a Kudanci.”
A ranar Laraba ce Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka amince da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro; Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin Hafsan Sojan Ƙasa; Rear Admiral Idi Abbas Hafsan Sojan Ruwa; Air Marshall Kennedy Aneke Hafsan Sojan Sama; da Manjo Janar Emmanuel Undiendeye a matsayin Shugaban Tattara Bayanai na Soja.
“Ba zai yiwu mu ƙyale wannan sabuwar barazanar ta ci gaba ba. Dole ne mu ɗauki mataki da wuri. Mu sare kan macijin.
“’Yan Najeriya suna sa rana ganin sakamako, saboda haka babu wani uzuri da za su karɓa. Ina kuma kira da ku kasance masu dabaru da hangen nesa da kuma jarumta.
“Mu kasance mun tari hanzarin duk waɗanda ke neman tayar da zaune tsaye a ƙasarmu,” in ji Tinubu.
Yayin bikin, an ƙara wa Olufemi Oluyede muƙami zuwa Janar, Waidi Shaibu zuwa Laftanar Janar, Idi Abbas zuwa Vice Admiral, da Kevin Aneke zuwa Air Vice marshall, da kuma Emmanuel Undiendeye zuwa Laftanar Janar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hafsoshin tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Dantsoho Ya Yaba Wa Ƙoƙarin Oyetola Na Dawo Da Nijeriya Tsarin Sufurin Jiragen Ruwa Na Duniya
“Dawo Nijeriya a cikin rukunin na C a kungiyar ta IMO hakan ya nuna irin zagewar kasar nan na iya tafiyar da tsare-tsare da bin ka’idojin gudanar da sufurin Jiragen Ruwa da wanzar da tsaro da kuma samar da kyakyawan yanayi, ga fannin,” Inji Dantsoho.
“Wannan ci gaban, ba wai ga kasar nan ne kadai ba, har da ma ci gaban daukacin Afirka ta Yamma musamman a bangaren kara bunkasa ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a nahiyar da samar da hanyoyin kara habaka safarar kaya zuwa ketare da kuma kara bunkasa fannin tattalin arziki na teku'” A cewar shugaban.
“Nijeriya a yau, ta kai wani babban mataki da duniya ke sauraronta a saboda haka, ina kara taya Nijeriya da hukumar ta NPA kan wannan nasarar da ta samu'” Inji Dantsoho.
Shugaban ya kuma yabawa ministan bunkasa tattalin arziki Dakta Adegboyega Oyetola, musamman kan jajircewarsa, wajen daga matsayin kasar nan, a fannin kula da lafiyar da sufurin Jiragen Ruwa na kasa
r nan.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA