Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai
Published: 30th, October 2025 GMT
Xi ya kuma bayyana cewa, saboda bambancin yanayin kasashen Sin da Amurka, ba makawa akwai wasu sabanin ra’ayi, amma baya ga kalubale da takara, ya kamata shugabannin biyu su rike shugabanci, da kuma samar da alkibla mai dacewa, don ba da damar bunkasa dangantakar Sin da Amurka ta ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali.
A nasa bangare, Trump ya ce, yana farin ciki matuka bisa haduwa da dadadden abokinsa. Ya ce, “Za mu tattauna da mai girma shugaban kasar Sin Xi Jinping. Ina da imanin cewa, mun riga mun kai ga cimma matsaya daya, kuma za mu cimma karin matsaya a nan gaba. Xi Jinping wani sahihin shugaba ne mai kima.”
Ya kuma ce, “Ba shakka kasashen biyu za su kafa nagartacciyar hulda ta dogon lokaci, ina kuma farin cikin hakan tare da shugaba Xi.”
Shugabannin biyu sun shafe sa’a 1 da mintuna 40 suna tattaunwa.
A wannan rana kuma, shugaban kasar Xi Jinping ya isa kasar Korea ta Kudu, domin halartar taron kwarya-kwarya na shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Asia da Pasifik (APEC) karo na 32, bisa gayyatar da shugaban kasar Korea ta Kudu Lee Jae-myung ya yi masa.(Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An kashe mutum 2 a rikicin limancin masallacin Juma’a a Taraba
Rikici tsakanin bangarori biyu a garin Donga na Jihar Taraba, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a kan limancin masallacin Juma’a na garin.
Bayanai sun nuna baya ga mutanen da suka mutu, wasu da dama sun jikkata kuma an lalata dukiyoyi.
An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a KadunaRikicin, kamar yadda Aminiya ta gano, ya faru ne a ranar Talata kan limancin masallacin Juma’a na garin da ke gaban fadar Sarkin Donga.
Wata majiya daga garin ta shaida wa wakilinmu cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani tsakanin kungiyoyi biyu na al’ummar Musulmi a garin kan wanda ya kamata ya zama limami na masallacin na Juma’a.
An ce sabanin ya rikide zuwa rikici mai zafi tsakanin bangarorin biyu, wanda ya haifar da mutuwar mutane biyu da kuma jikkatar wasu da dama.
Majiyar ta kara da cewa jami’an tsaro ciki har da sojoji sun isa yankin domin shawo kan halin da ake ciki.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai daga wayar ko amsa sakon da wakilinmu ya aike masa ba dangane da lamarin.