HKI Tana Cigaba Da Yi Wa Mutanen Gaza Kisan Kiyashi
Published: 10th, July 2025 GMT
Sojojin Sahayoniya suna ci gaba da yi wa mutane Gaza kisan kiyashi a kwana na 643 a jere.
Sojojin sahayoniyar suna amfani da dukkanin kayan yaki da su ka hada jiragen masa masu matuki da marasa matuki, da kuma manyan bindigogi.
Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare da tankokin yaki bayan kutsawarsu cikin yankin “Bi’irut-Turki” da “maslakh” dake kudancin Khan-Yunus.
Majiyar Falasdinawa ta tabbatar da shahadar mutane 16, da su ka hada mata da kananan yara a wuruin da suke jiran karbar abincin agaji a shataletalen al-Dhayyarah, a Deir-Balah dake tsakiyar birnin Gaza.
A gabashin birnin Gaza kuwa, sojojin mamayar sun kara rusa gidaje masu yawa, da ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 4 a cikin iyalai guda na Abu Jild.
Har ila yau, majiyar ta ce, wani karamin yaro mai suna Yusuf Hassan al-Ammur ya yi shahada sanadiyyar raunukan da ya samu a jiya da ‘yan sahayoniyar su ka kai hare-haren da su ka kwantar da shahidai 4.
A sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” kuwa dake tsakiyar Gaza wani Bafalasdine mai suna; Abduljalil Khitab, da Akram al-Dairawi, sun yi shahada saboda harin da sojojin mamayar su ka kai wa motar da suke ciki. A tsakiyar daren jiya ma dai wasu Falasdinawan 5 su ka yi shahada a yankin Mawasi dake yammacin Khan-Yunus.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.
Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp