Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100
Published: 30th, October 2025 GMT
Hukumar agaji a yankin Gaza ta sanar da cewa fiye da mutane 100 ne su ka yi shahada.
Hukumar ta agaji ta bayyana abinda HKI take yi na ci gaba da kai wa Gaza hare-hare a matsayin keta tsagaita wuta. Su kuwa kungiyoyin gwgawarmaya a yankin sun bayyana abinda yake faruwwa da cewa yana da hatsarin gaske.
Ma’aikatar kiwon lafiya a yankin Gaza, ta sanar da cewa; a cikin shahidan da akwai kananan yara 46, sai kuma wasu 253 da su ka jikkata.
Asibitin “ Nasir” ya sanar da cewa wasu mutane 20 sun yi shahada sanadiyyar hare-haren sojojin HKI a birnin Khan-Yunus dake kudancin birnin Gaza.
Wasu jerin hare-haren ‘yan sahayoniyar sun shafi gidajen mutane a Khan-Yunus da Deir-Balah da Gaza. Sun kuwa yi amfani ne da jiragen sama marasa matuki wajen kai hare-haren. An sami shahidai 3, a yankin sai kuma wasu Karin shahidan 4 sansanin ‘yan hijira dake “Ardh-Insan” a gabas da asibitin Aqsa dake Deir-Balah.
Sojojin HKI sun kuma kai wani hari da jirgin sama maras matuki akan sansnain ‘yan hijira a dandalin garin Deir-Balah da ya ci rayukan falasdinawa 4. A yankin al-mawasi dake yammacin Khan-Yunus, wasu Faalsdinawan 5 sun yi shahada.
A baya kadan, ofishin hukumar Gaza ya sanar da cewa sau 127 HKI ta keta yarjejeniyar tsagaita wutar yaki, wacce ta fara aiki a ranar 10 ga watan nan na Oktoba mai karewa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Ta Hana Marubuci Dan Nigeria Wole Soyinka Izinin Shiga Amurka October 30, 2025 Pakistan Tayi Barazanar Daukar Mataki Bayan Rushewar Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta Da Afghanistan. October 29, 2025 IRS: Sanya Sabbin Takunkumi Kan Kasar Iran Zai Haifar Da Mummunan Sakamakon A Yankin October 29, 2025 An saka dokar Ta Baci Bayan Barkewar Zanga-zanga A Zaben Shugaban Kasar Tanzaniya October 29, 2025 Majalisar Dattawa A Najeriya Ta Tantance Sabbin Manyan Hafsoshin Sojin Kasar October 29, 2025 Shugaban kasar Iran Ya Taya Takwaransa Na Turkiya Murnar Zayowar Ranar Samun Yancin Kai October 29, 2025 Bayan Kwace Birnin Al-Fasher Kungiyar Rapid Support Forces Suna Ci Zarafin Al’Umma October 29, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Ake Kaiwa Fararen Hula A Birnin El-Fasher Na Sudan October 29, 2025 Jakadan Iran A MDD Ya Jaddada Kawo Karshen Takunkumin Amurka Kan Kasar Cuba October 29, 2025 Jami’ar MDD Ta Musamman A Falasdinu Ta Soki Shirin Trump Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sanar da cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Larijani: Dangantakar Iran da Pakistan na iya komawa babban hadin gwiwa a tsakaninsu
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran Ali Larijani (SNSC) ya ce dangantakar da ke tsakanin Tehran da Islamabad tana habaka, kuma za ta iya kaiwa matsayin babban hadin gwiwa na din-din-din.
Ali Larijani, a yayin da yake yin wata ganawa da Ministan Harkokin Cikin Gida na Pakistan Syed Mohsin Naqvi a wannan Talata a birnin Tehran, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar ƙasashen biyu a fannin tattalin arziki.
Ya nuna yarjejeniyar dabarun da aka cimma a cikin kwanakin nan tsakanin Pakistan da Saudiyya, a matsayin mataki mai kyau kuma na hikima, wanda yake da tasiri matuka ga irin barazana da kasashen musulmi sue fuskata daga makiya.
Larijani ya ce yanayin yankin a yau yana cike da ƙalubale daga maƙiya, wanda ke buƙatar aikin hadin gwiwa mai ma’ana, mai tsari, da kuma cikakken aiki tsakanin ƙasashen Musulmi.
Larijani, wanda kuma yake aiki a matsayin mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya jaddada buƙatar zurfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro, siyasa, da kuma musamman fannin tattalin arziki.
Ya kuma gode wa gwamnatin Pakistan saboda matsayinta a lokacin harin kwanaki 12 da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a watan Yuni, yana mai cewa hakan shaida ce ta fahimtar juna mai zurfi da ka e tsakanin kasashen biyu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iraki: Al-Sudani ya kirayi Irakawa da suka kare kundin tsarin Mulki ta hanyar fitowa zabe October 29, 2025 Abiy Ahmed: Habasha na bukatar sulhu kan rikicin teku tsakaninta da Eritrea October 29, 2025 Hare-haren Isra’ila Sun Kashe Mutane fiye da 60 a Gaza October 29, 2025 Senegal ta sake gano wasu shaidu kan kisan gillar da aka yi a lokacin mulkin mallaka October 29, 2025 An bude taron ministocin cikin gida na kungiyar ECO October 28, 2025 Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku a Yammacin Kogin Jordan October 28, 2025 Hamas : Netanyahu Yana kokarin wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta October 28, 2025 China za ta dauki mataki idan takunkuman Iran sun shafi muradunta October 28, 2025 Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji Ukraine October 28, 2025 Pezeshkian: Hadin Kai A Tsakanin Kasashen Gabas Ta Tsakiya Ba Zabi Ba Ne, Amma Dole Ne October 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci