Aminiya:
2025-07-08@20:42:44 GMT

‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’

Published: 8th, July 2025 GMT

Tsohon Ministan Sufuri, Idris Umar, ya bayyana cewa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ce za ta ceto Najeriya daga halin da take ciki, tare da mayar da APC jam’iyyar adawa a Zaɓen 2027.

Yayin wani taron haɗin gwiwar jam’iyyu na adawa a Gombe, an amince da amfani da ADC a matsayin dandalin siyasa na bai ɗaya domin fuskantar zaɓen 2027.

Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC NAJERIYA A YAU: Sarƙaƙiyar da ke gaban Haɗakar ADC: Atiku ko Peter Obi

Taron ya gudana a Shugleez Event Centre wanda ya samu halartar fitattun ‘yan adawa daga sassa daban-daban na jihar.

Idris ya ce za su yi haɗakar ce ba wai kawai don karɓar mulki ba, sai dai domin ceton ƙasa da talakawa daga matsin tattalin arziƙi da rashin shugabanci nagari.

Shugaban ADC na jihar, Auwal Abba Barde, ya ce jam’iyyar na samun karɓuwa daga sabbin mambobi tare da tabbatar musu da wakilci

Aminiya ta ruwaito cewa an kafa kwamitin rajistar sabbin mambobi ƙarƙashin tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe, John Lazarus Yoriyo, da AVM Adamu Fura a matsayin mataimaki.

Tsohon shugaban matasan APC, Sunusi Abdullahi Ataka, ya ce haɗakar za ta yi tasiri wajen karɓar mulki a Gombe da Najeriya gaba ɗaya.

Wasu daga cikin mahalarta sun haɗa da wakilin Farfesa Isa Ali Pantami, Abubakar Abubakar BD, da sauran jiga-jigai na jam’iyyar ADC.

Bayanai sun ce a yanzu haka jam’iyyar ADC da ’yan haɗaka da wasu jagororin ’yan hamayya suka dunƙule a ƙarƙashin inuwarta ta fara karɓe tsarin jagorancin jam’iyyar PDP a jihohin Yobe da Adamawa da kuma Gombe.

Sun ce an samu ’yan PDP da dama da suka sauya sheƙa zuwa ADC, ciki har da waɗanda suka riƙe manyan muƙamai a baya.

A Jihar Adamawa wasu daga cikin ƙusoshin jam’iyyar da suka riƙe mukamai a matakai daban daban na jiha tuni suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ’yan hadaka ta ADC inda kawo yanzu shugabannin jami’yyar PDP a ƙananan hukumomi goma a cikin jihar suka fice daga cikin jam’iyyar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: adawa Idris Umar jihar Gombe

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban

Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka halaka yayin da wasu 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da aka kai musu a arewacin Gaza

Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka sheka lahira sannan wasu akalla 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da ‘yan gwagwarmaya suka kai a Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. Har yanzu wani sojan Isra’ila ya bace kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka ruwaito.

Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da s’yan gwagwarmaya suka tayar da bam a cikin wata motar sojin Isra’ila mai sulke dauke da sojoji, sannan suka nufi wani mutum-mutumi da ke dauke da harsashi da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi.

Hare-haren dai sun auka ne kan dakarun ceto na Isra’ila da suka garzaya zuwa wurin, yayin da mazauna birnin Ashkelon suka ji karar fashewar wani babban bam, a cewar shafukan yanar gizo na Isra’ila, inda suka ce daya daga cikin wadanda suka jikkata wani babban jami’i ne.

Sojojin da aka kai wa harin na sashen injiniyan Yahalom ne, wanda ke da alhakin yin tarko da kuma tayar da bama-bamai a gidajen Falasdinawa a zirin Gaza, a cewar wakilin Al Jazeera na Falasdinu, Najwan Samri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ɓarayin babura a Gombe
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • An ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutum 38,000 a Gombe
  • China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga Kasashen BRICS
  • Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Ambaliyar Texas Ya Haura 80
  • Elon Musk zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Amurka
  • Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC
  • Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC
  • ‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027