Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya
Published: 30th, October 2025 GMT
Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci Ma’aikatar Yakin da ta ci gaba da gwajin makaman nukiliya nan take, shawara da tauni ta tsorata masu fafutukar yaki da irin wannan manufa.
A cikin wani sako da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social yau Alhamis, Trump ya bayyana cewa ya bayar da umarnin “saboda shirye-shiryen tantancewa da wasu kasashe suke yi.
Shugaban Amurka ya bayyana Rasha da China a matsayin kasashe na biyu da na uku na duniya masu karfin makamman nukiliya, bi da bi, yana mai tabbatar da cewa idan Washington ba ta ci gaba da gwajin makaman nukiliya ba, wadannan kasashe za su cimma ta nan da ” shekaru biyar.”
Ana sa ran tsarin gwajin zai samar da bayanai kan ayyukan sabbin makaman yaki da kuma amincin tarin makaman da suka tsufa.
Matakin na Trump shi ne wani kira na kai tsaye da Amurka ta yi na ci gaba da gwajin nukiliya tun bayan gwajin da Washington ta yi na karshe a shekarar 1992.
Masu suka sun yi gargadin cewa sake fara gwajin nukiliya na kai tsaye zai iya kawo karshen shekaru da dama na kokarin hana yaduwa da kuma haifar da tarin gwaje-gwajen ramuwar gayya a duk faɗin duniya, wanda hakan zai wargaza Yarjejeniyar Hana Gwajin Makaman nukiliya (CTBT).
A bara, wani rahoto ya nuna cewa Amurka na shirin kashe ɗaruruwan biliyoyin daloli don sabunta makaman nukiliyarta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: gwajin makaman nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC
Lauyan ICPC, Osuobeni Akponimisingha, ya gabatar da ƙarar neman a kwace kuɗin, yana sanar da kotun cewa, ICPC ta bi umarnin wucin gadi na kwace dalolin da ta yi a baya. Ya ce, an buga sanarwa ta jama’a inda aka gayyaci duk wani mutum wanda yake ganin akwai dalilin da zai hana ko kuma bai kamata a kwace kudin ba har abada, amma babu wanda ya amsa.
“Saboda haka, muna neman a ba da umarnin a kwace kudin har abada a mayar da su ga Gwamnatin Tarayya, saboda bin umarnin wucin gadi kuma babu wanda ya nuna adawa da hukuncin,” in ji Akponimisingha ga kotun.
Hukuncin ya biyo bayan umarnin wucin gadi da kotun ta bayar a ranar 30 ga Disamba, 2024, domin amsa bukatar da ICPC da Ma’aikatar tsaron farin kaya ta cikin gida (DSS) suka gabatar tare.
Takardar neman izinin, mai lamba FHC/ABJ/CS/1846/2024, kuma Usman Dauda, Daraktan Ayyukan Shari’a na DSS ya sanya wa hannu, ta nuna cewa an gano kudaden ne a lokacin bincike a gidan Dr. Ali da ke Kano.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA