2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo
Published: 9th, July 2025 GMT
Tsohon jigo a Jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya ce dole ADC ta tsayar da ɗan Arewa takara idan tana son ta kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
A cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Okonkwo, ya ce idan ADC ta tsayar da ɗan Kudu takara, Tinubu zai sake lashe zaɓe ba tare da wata tangarɗa ba.
Ya ce dole ne ’yan adawa su yi aiki da hikima da dabaru idan suna son yin nasara.
“Shirina a wannan karon shi ne zan goyi bayan ɗan Arewa a 2027,” in ji shi.
Ya ce wannan ɗan takarar dole ne ya kasance mutum mai farin jini a Arewa.
Ya ambaci sunan Atiku Abubakar da Aminu Tambuwal a matsayin misali na mutanen da ke da farin jini a yankin.
“Mutumin dole ne ya cancanta. Idan ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙasa ko kusa da hakan, to hakan zai ƙara wa tafiyar armashi.
“Idan ya haɗu da ɗan Kudu a matsayin mataimaki, to hakan zai taimaka sosai,” in ji Okonkwo.
Ya bayyana shugabancin Tinubu a matsayin “mara amfani,” inda ya ce ƙarfin ɗan Arewa ne kawai zai iya kawowa takarar Tinubu cikas.
Ya yi gargaɗin cewa tsayar da ɗan Kudu takara a jam’iyyar zai sa Tinubu ya lashe zaben cikin sauƙi.
“Idan ka tsayar da ɗan Kudu domin yin takara da Tinubu, wanda shi ma ɗan Kudu ne, to zai lashe zaɓe cikin sauƙi.”
“Idan aka kawo ɗan Kudu Maso Gabas, ko da ya yi nasara, za su murɗe zaɓen a hannunsa ,” in ji shi.
Ya bayyana cewa a siyasar Najeriya, sai ka samu goyon bayan “tsari” kafin ka iya kare nasararka.
Ya ce yankin Kudu Maso Yamma bai taɓa fafatawa da shugaban ƙasa mai ci ba saboda sun san dabarar siyasa.
Ya sake jaddada cewa Peter Obi ne ya lashe zaɓen 2023, amma an ƙwace masa.
Ya ce hakan na iya sake faruwa idan ba a shirya da kyau ba.
“Amma idan ɗan Arewa ne ya ci, babu wanda zai murɗe masa ko a ce ya sauka domin ba su fito daga yankin ɗaya da Tinubu ba,” in ji shi.
Okonkwo, ya fice daga jam’iyyar LP a watan Yulin 2024 saboda rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar ke fama da shi.
Yanzu da ’yan adawa suka haɗu ƙarƙashin jam’iyyar ADC, yana fatan za su iya ƙirƙiro tafiya mai ƙarfi domin tukarar zaɓen 2027.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Siyasa Zaɓe tsayar da ɗan da ɗan Kudu a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙungiyar Al’ummar Igbo Ta Ohanaeze Ndigbo Ta Ce Tinubu Ya Fi Ƙarfin ‘Yan Jam’iyyar Haɗaka Ta ADC
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp