Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta
Published: 30th, October 2025 GMT
Iran ta yi ikirarin cewa Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya “san”sarai da cewa shirin nukiliyar kasar na lumana ne, don haka ya kamata ya guji yin “kalamai marasa tushe” kan lamarin.
A wata hira da ya yi da tashar Al Jazeera, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa kalaman da Rafael Grossi ya yi a baya sun share fagen ayyukan ta’addanci da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka yi wa Iran a watan Yunin da ya gabata.
Ya kamata Darakta Janar na IAEA ya guji yin kalamai marasa tushe game da shirin nukiliya na Iran, in ji shi.
Rafael Grossi ya bayyana a ranar Laraba cewa IAEA ta gano kwanan nan da sake dawowa da ayyuka a wuraren nukiliya na Iran,” bayan ya amince cewa kasar ba ta nuna alamun kara wadatar da uranium ba.
A cikin wani rahoto na sirri da aka gabatar wa Kwamitin Gwamnonin IAEA a ranar 31 ga Mayu, 2025, Babban Daraktan IAEA ya yi iƙirarin cewa “Iran ta gaza bayyana ayyukanta na nukiliya a wurare uku da ba a bayyana ba” kuma ta bayyana damuwa game da tarin sinadarin uranium da ta wadatar zuwa kashi 60%.
A cewar jami’an Iran, rahoton Grossi game da shirin nukiliya na Tehran ya share fagen kai hari ga Isra’ila kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A karshen watan Yuni ne, Majalisar Tsaron Iran ta amince da wani kudiri da majalisar dokokin kasar ta zartar wanda ya dakatar da haɗin gwiwa da hukumar ta IAEA.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Zata Dauki Bakoncin Taro Dangane Da Kasar Afganistan Da Tsaron Yankin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baqai ya bada sanarwan cewa Tehran zata dauki bakoncin wasu kasashen yankin don tattaunawa dangane da harkokin tsaro a kasashen yankin musamman tsakanin Afganisatan da Pakistan.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghae na fadar haka a safiyar yau Jumma’a ya kuma kara da cewa kafin haka kasashen Qatar, Turkiya da Saudiya sun yi kokarin sasanta kasashen Afganistan da Pakisatan dangane da rikice-rikicen da ke aukuwa tsakanin kasashen biyu a cikin yan watannin da suka gabata.
Ya ce gwamnatin kasar Iran tana son ganin an kawo karshen duk wata rigima tsakanin kasashen yankin saboda tana shafar al-amura da dama a yankin.
Labarin ya kara da cewa taron wanda za’a gudanar a a mako mai zuwa zai sami halattan wakilai daga kasashen Afghanistan Pakistan, Tajikistan, Uzbekistan, Turkmenistan, China da Russia.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut December 12, 2025 Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba December 12, 2025 Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026 December 12, 2025 Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci