Gwamnatin Gombe ta fara tantance ma’aikata don kawar da na bogi
Published: 29th, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe, ta fara aikin tantance ma’aikata sama da 7,000 ta hanyar Intanet domin tabbatar da bayanansu da kuma kawar da ma’aikatan bogi.
Shugabar Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar (CSC), Hajiya Rabi Shu’aibu Jimeta, wacce ke jagorantar aikin, ta ce wannan shiri na nufin tabbatar da sahihancin bayanan ma’aikata.
Ta bayyana cewa za a kammala aikin cikin makonni takwas, kuma duk ma’aikatan da abin ya shafa za a ɗauki bayanansu domin sauƙaƙa samun bayanai.
Hajiya Jimeta, ta ce an keɓe ma’aikatan shari’a, hukumar malamai (Teachers Service Commission), da ma’aikatan lafiya, saboda hukumominsu na da tsarin tantancewa nasu.
Ta ƙara da cewa aikin na daga cikin shirin gyaran ma’aikata da gwamnatin jihar ke aiwatarwa domin gano ma’aikatan bogi da kuma waɗanda suka wuce lokacin ritaya.
“Bayan kammala aikin, za mu bai wa gwamnati shawara ta ɗauki sabbin ma’aikata da suka cancanta domin maye gurbin giɓin da ake da shi,” in ji ta.
A nasa jawabin, shugaban Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) reshen Gombe, Kwamared Yusuf Ash Bello, ya yaba da matakin.
Ya ce aikin na da muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya da inganta tsarin ma’aikata.
“Muna goyon bayan wannan aiki saboda zai samar da sahihin adadin ma’aikatan gwamnati. Ba za mu ci gaba da dogaro da bayanan bogi ko takardun bogi ba,” in ji Bello.
Wasu daga cikin ma’aikatan da aka riga aka tantance sun nuna farin cikinsu, inda suka bayyana cewa hakan zai taimaka wajen inganta hakkokinsu da ƙarin girma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tantancewa Tsari
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu
An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu.
Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai miliyoyin Naira.
APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar SayawaLokacin da aka fara sauraren shari’ar, lauya mai kare gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya ce sun shirya fara gabatar da shaidu, amma lauyoyin Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka nemi ƙarin lokaci, inda suka bayyana cewar ba a ba su wasu takardu ba.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu-Aliyu, ta umarci dukkanin ɓangarorin su kammala miƙa takardunsu kafin zaman kotun na gaba, sannan ta ɗage shari’ar zuwa 26 ga Nuwamba, 2025.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA