Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC
Published: 8th, July 2025 GMT
Jam’iyyar ADC ta zargin Fadar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinuba da shirya mana wata kutungwila mai hadarin gaske domin kawo cikas ga hadakar ’yan adawan da ke kara samun farin jini.
Sakataren Yada Labarai na ADC na Kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya ce a sakamakon haka gwamnatin APC a matakin kasa ta kira wani taron sirri tsakanin wasu manyan jami’an gwamnati da shugabbanin jam’iyyar ADC na jihohi da kuma kusoshinta daga yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Ya ci gaba da cewa, hadafin taron na su shi ne “kawo rudani a jam’iyyarmu, bayyana shugabanninta a matsayin haramtattu da kum kawar da ita daga manufofin da ta sanya a gaba, lura da karuwar yadda jam’iyyar take kara samun farin jini a tsakanin ’yan Najeriya
“Wannan shirin na karkatar da hankalin ciyamomin ADC na jihohi da jami’an gwamnati da ya kamata su mayar da hankali kan warware matsalar tsaron da saurannsu da suka addabi kasa, suke yi, ba komai ba ne face hari ga tsarin dimokuradiyya.“Daga haka ake fara samun kasa mai tsarin jam’iyya daya—ta hanyar barazaa,” in ji jami’in na ADC.
Ya ci gaba da cewa, “Hadar ADC ta rikita APC kuma yanzu ta bayyana cewa Gwamnatin Tiubu wadda ta rasu goyon bayan ’yan Najeriya ba za ta iya jure matsin da take ciki a sakamakon wannan hadaka da nagarta ba.“Amma kuma a maimakon ta gyara kurakurenta sai ta kare da kokarin amfani da tsohuwar dabararta ta kawo rudani a jam’iyyun adawa.”
Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ta ’yan Najeriya ce, wadanda suka gaji da karairayi da yaudara da kuncin rayuwa. Ta ’yan Najeriya ne masu burin dawo da martaba da kyakkyawan fata da kuma adalci a shugabanci. “Saboda haka ba za mu bar wasu tsirarun mutane masu kama-karya su mayar da kasar nan mai jam’iayya daya ba. Hallo kane a kan kowannenmu ya yaƙi hakan ta yadda ya kamata.”উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: adawa jam iyya yan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ko ɗansa zai naɗa shugaban INEC, APC sai ta faɗi zaɓen 2027 — Dalung
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce duk wani yunƙuri da Shugaba Bola Tinubu, zai yi ba zai hana jam’iyyar APC faɗuwa a zaɓen 2027 ba.
Yayin wata hira da aka yi da shi a Jos, a Jihar Filato, Dalung, ya ce ko da Tinubu zai naɗa ɗansa Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), ko matarsa ta zama Babbar Alƙalin Alƙalai ta Ƙasa, hakan ba zai taimaka wa APC ba.
Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a KanoYa ce gwamnatin APC ta gaza, kuma ta jefa ‘yan Najeriya cikin ƙunci da yunwa ta hanyar manufofinta marasa kan gado.
Dalung ya ce: “Ko duk gwamnonin jihohi 36 za su koma APC, kuma Tinubu ya naɗa ɗansa shugaban INEC, sai sun faɗi a 2027. Wannan karon tsakanin talakawa da gwamnati ne.”
Ya ƙara da cewa ‘yan Najeriya su shirya wa zaɓen 2027 domin ƙalubalantar gwamnatin Tinubu wadda ta jefa su cikin yunwa, talauci, da rashin adalci.
Dalung, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin mafakar muggan ‘yan siyasa, inda ya ce jam’iyyar ba ta da tsari ko aƙida, kuma yawaitar masu sauya sheƙa zuwa cikinta zai haddasa mata rikici nan ba da daɗewa ba.
Ya bayyana dalilin ficewarsa daga APC zuwa jam’iyyar SDP, inda ya ce taron da suka yi da Tinubu ya ba shi kunya, domin shugaban bai fahimci matsalolin da suka tattauna ba.
Dalung, ya kuma soki shugabannin siyasar Najeriya gaba ɗaya, inda ya bayyana cewa suna tafiyar da ƙasar ne ta hanyar son kai.