Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026
Published: 30th, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da taron sauraron ra’ayoyi jama’a kan shirye-shiryen tsara kasafin kuɗin shekarar 2026 a wani yunƙuri na jaddada ƙudirinta na gudanar da mulki cikin gaskiya da haɗin kai.
Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna jajircewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya wajen tabbatar da cewa ra’ayoyin jama’a na taka muhimmiyar rawa a tsara kasafin kuɗi da aiwatar da shi.
Ya ce tattaunawar ta bai wa gwamnati damar haɗa kai da sarakunan gargajiya, mata, matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki, domin bayar da shawarwari kan muhimman fannoni kamar ilimi, lafiya, noma da gine-gine, da za su amfanar da al’umma baki ɗaya.
Dakta Jatau ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta samu ci gaba wajen alkinta kuɗaɗe cikin tsari da gaskiya, wanda hakan ya sa Gombe ke samun matsayi mai kyau a ɓangaren ingantaccen gudanar da kuɗi da sauƙin kasuwanci a Najeriya.
“Kasafin kuɗin 2026 zai mai da hankali ne kan ci gaba da ayyukan da ake yi, tare da ƙara zuba jari a muhimman fannoni, da tabbatar da daidaito da manufofin ci gaban ƙasa da na duniya,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Kasafi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Alhaji Salihu Baba Alkali, ya bayyana taron a matsayin wata hanya ta buɗe ƙofa tsakanin gwamnati da jama’a domin samun fahimta da amincewa.
Ya buƙaci mahalarta taron da su bayar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen samar da kasafin kuɗin da zai kasance mai ɗorewa kuma mai amfani ga kowa da kowa.
Kwamishinan ya kuma gode wa mahalartan bisa yadda suka bayar da gudunmawa, yana mai tabbatar da cewa za a yi la’akari da shawarwarinsu a cikin tsarin ƙarshe na kasafin kuɗin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Gombe Ra ayoyi
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe mai ciki da ɗanta a Kano
Al’ummar unguwar Sheka Sabuwar Gandu da ke Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano, sun shiga fargaba, bayan wasu da ba a san ko su waye ba, suka kashe wata mai ciki da ɗanta ɗan wata18 a duniya.
An tabbatar da faruwar lamarin da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da mijin matar ya dawo gida daga aiki ya tarar ƙofar gidan a kulle.
Hafsan sojin ƙasa ya buƙaci sabbin dakaru su zama masu kishin ƙasa An kashe mutum 11 da jikkata wasu 29 a bikin Yahudawa a OstireliyaA cewar maƙwabtan matar, bayan mijin ya tambayi jama’a a unguwar, sai ya shiga gidan, inda ya tarar da gawar matarsa da ta ɗanta.
Daga nan ne al’ummar unguwar suka sanar da hukumomin tsaro.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban jama’a aunguwar, Ahmad Sani, ya ce jama’a sun shiga firgici da tashin hankali matuƙa.
Ya koka da rashin tsaro a yankin, inda ya bayyana cewa duk da gina ofishin ’yan sanda a unguwar, har yanzu ba a turo jami’an tsaro da za su kula da shi ba.
“Dukkanin al’ummar unguwar sun shiga ruɗani. Ba a taɓa samun irin wannan abu ba. Muna cikin damuwa saboda babu jami’an tsaro a nan,” in ji shi.
Ya roƙi Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, da ya ɗauki matakin gaggawa wajen inganta tsaro a yankin domin hana sake faruwar hakan.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba zai ce komai ba domin rundunar na gudanar da bincike.
A halin yanzu, mazauna yankin sun buƙaci hukumomin tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata laifin.