Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin Gusau
Published: 25th, July 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara.
Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71.
An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a KanoMai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.
Ya ce Sarkin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa don hidimta wa al’ummarsa.
Shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sarkin babban rashi ne, ba wai kawai ga mutanen masarautarsa ba, har da ƙasa baki ɗaya.
Ya yaba da jajircewarsa, kyakkyawan shugabancin da sadaukarwarsa ga jama’a.
Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin Jihar Zamfara, mutanen jihar, da kuma iyalan marigayin.
Ya roƙi Allah Ya jiƙan Sarkin, Ya kuma yafe masa kurakuransa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: rasuwa Sarkin Gusau ta aziyya
এছাড়াও পড়ুন:
Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa
An cimma matsaya kan zaɓensa bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC.
Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar za su tabbatar da naɗinsa a yau Alhamis.
Farfesa Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da suke da alhakin riƙe kujerar shugabancin jam’iyyar.
Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar sun ce kasancewarsa Kirista zai taimaka wajen daidaita shugabanci, duba da cewa shugaban ƙasa da mataimakinsa Musulmai ne.
Shugabannin jam’iyyar na fatan Farfesa Yilwatda zai kawo sabon salo, tare da haɗa kan jam’iyyar kafin tunkarar zaɓe mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp