Kungiyar ‘Yan Jaridar Jihar Zamfara Ta Gudanar Zaben Sabbin Shuganni.
Published: 13th, July 2025 GMT
A bisa umarnin sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ, an yi nasarar gudanar da zaben majalisar jihar Zamfara a ranar Asabar din da ta gabata cikin kwanciyar hankali da lumana, inda aka dawo da dukkan mukamai ba tare da hamayya ba.
Mukamin daya tilo da aka fara takaddama a kai ya sa daya daga cikin masu neman takarar, Rabi Yusuf ta janye bisa radin kanta, wanda a hukumance ta sauka ta hanyar mika takarda ga kwamitin tantancewa, tare da aika kwafin ga mataimakin shugaban shiyyar da Sakatare.
Wakilai daga Sakatariyar NUJ ta kasa ne suka jagoranci gudanar da zaben da kuma kaddamar da taron wanda suka hada da mataimakin shugaban shiyyar A, Muhammad Tukur Umar da sakataren shiyyar Abdulrazak Bello Kaura.
Wadanda aka zaba ba tare da hamayya ba, kuma aka rantsar da su sune Ibrahim Musa Maizare na Jaridar Legacy a matsayin Shugaban, Mataimakin Shugaba, Halliru MB Umar na NTA da Sakatare Ibrahim Ahmad Gada na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya – NAN.
Sauran sun hada da Mataimakin Sakatare, Jamilu Sani Tsafe na Jaridar Legacy, Ma’ajin Nafisa Abubakar Kanoma ta Gidan Rediyon Zamfara, Sakataren Kudi na FRCN Pride FM, Surajo Muhammad, da kuma Auditor Ibrahim Muhammad na Jaridar Legacy.
Mataimakin shugaban shiyyar Muhammad Tukur Umar ne ya jagoranci bikin kaddamarwar, inda ya umurci sakataren shiyya da ya gudanar da rantsuwar ga sabbin jami’an da aka zaba.
Kafin rantsar da shi, Sakatare da Ma’aji mai barin gado sun gabatar da rahotonsu a Sakatariyar Majalisar, bayan an rusa majalisar zartaswar da ta gabata a hukumance domin share fagen gudanar da sabon shugabanci.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban na shiyyar, ya bukaci sabbin jami’an da aka kaddamar da su kiyaye kundin tsarin mulkin NUJ, ba da nuna son rai ba da kuma karfafa ci gaban aikin jarida.
Ya jaddada mahimmancin horarwa akai-akai, dabarun inganta iyawa, da kuma saurin musayar bayanai tsakanin membobin.
Ya kuma bukaci ‘yan jarida a fadin jihar da su samar da hadin kai, mutunta juna, da kuma biyan kudaden shiga a kan lokaci, tare da bayyana su a matsayin wani muhimmin nauyi da ya rataya a wuyan kungiyar.
A wata sanarwa da sakataren shiyyar na NUJ, Abdulrazak Bello Kaura ya fitar ya bayyana zaben da aka gudanar cikin lumana
A jawabinsa na amince da zabin Shugaban kungiyar, Ibrahim Musa Maizare, ya yi alkawarin samar da jagoranci na bai daya tare da sabunta kudurin ci gaban kungiyar NUJ Zamfara ta kowane fanni.
Aminu Dalhatu/Gusau
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Zamfara da Sakatare
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Gagarumar Zanga Zangar Goyon Bayan Falasdinawa A Australia Da Indonasia
Duban dubatan mutane sun gudanar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa da kuma yin tir da kokarin samar da huldar jakadanci da HKI a maida kome kamar ba abinda ya faru. Sun kuma bayyana tsagaita wutan da aka samar da Hamas tana tangal tangal saboda tun farko ba’a gina shi kan yadda zata dore ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zanga suna cewa, wannan sulhun da kasashen yamma suka kulla da Hamas wani makirci ne na kara samun iko kasashen musulmi da ma wasu kasashen wadanda ban a musulmi ba.
Sun kuma bayyana cewa, bayan shekaru biyu da kissan kiyashi sun samar da abinda suka kira sulhu ne na wani lokaci, amma zaman lafiya ba zata taba dorewa ba sai an kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta kuma mai cikekken iko.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa October 14, 2025 Mahalarta Taron ‘Sherm-Sheikh” Sun Rattaba Hannu Akan Yarjejeniyar Zaman Lafiya October 14, 2025 MDD: Mutane 300,000 Su Ka Gudu Daga Sudan Ta Kudu A 2025 October 14, 2025 Iran Ta Gabatar Da Shawarar Kulla Yarjejeniyar Tausayawa A Tsakanin Matan Duniya October 14, 2025 Larijani: Gagarumar Tarbar Da Aka Yi Wa Fursunonin Falasdinawa Ta Nuna Hakikanin Wanda Ya Sami Nasara October 14, 2025 Hamas Ta Mika Yahudawa 7 Daga Cikin 20 Da ke Hannunta Ga Kungiyar Red Cross October 13, 2025 Iran: Kakabawa Kasa Mai Makwabta 16 Takunkumi Ba Abu Ne Mai Sauki Ba. October 13, 2025 An Gano Gawarwaki 323 Karkashin Burabutsai Bayan Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 13, 2025 Tehran Ta yi Gargadi Game Da Barazanar Yaduwar Fadan Iyakar Afghanisatan Da Pakistan. October 13, 2025 Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin Gargadi A Kasa Baki Daya . October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci