Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti
Published: 31st, October 2025 GMT
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta naɗa Luciano Spalletti a matsayin sabon kociya bayan sallamar Igor Tudor da ta yi a farkon makon nan.
Juventus ta ƙulla yarjejeniya da tsohon kociyan na Inter Milan da Roma da Udinese da Zenit St Petersburg da kuma tawagar ƙasar Italiya, har zuwa ƙarshen wannan kakar, yayin da take fatan samu gurbin zuwa gasar Kofin Zakarun Turai ta Champions League ta baɗi.                
      
				
Spalletti, shi ne kociyan da ya jagoranci Napoli wajen lashe gasar Serie A a 2023, wadda ita ce karon farko cikin shekaru 33, inda a yanzu ake fatan zai ƙara daidaita Juventus da ke fama da rashin katabus da matsalolin kuɗi tun daga 2022.
Spalletti, wanda aka sani da ƙwarewa wajen gina ƙungiya mai ƙarfi, ya dawo horaswa bayan gazawar da ya yi a matsayin kociyan Italiya a gasar Euro 2024, da kuma shan kashi a hannun Norway yayin wasan farko na neman tikitin Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Zuwa yanzu dai Juventus tana matsayi na bakwai a gasar Serie A da tazarar maki shida tsakaninta da Napoli da ke saman tebur, inda wasan farko da Spalletti mai shekaru 66 zai ja ragama shi ne da Cremonese.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Italiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15
Masana sun bayyana cewa wannan sabon haraji zai iya sa wa farashin mai ya tashi.
Gwamnati ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na ƙara samun kuɗaɗen shiga da rage yawan kashe kuɗi wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba