‘Abin da zai sa APC ba za ta taɓa mantawa da Ganduje ba’
Published: 9th, July 2025 GMT
Aminu Dahiru Ahmad, hadimin tsohon shugaban jam’iyar APC na kasa, Abudllahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar za ta gane ta yi kuskure kan saukarsa daga shugabancin.
A wata doguwar wasika da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana takaicinsa kan rashin nuna wa Ganduje halasci, duk da irin ci gaban da ya kawo jam’iyar wanda ya ce ba a taba samun makamancinsa ba.
“Tarihin APC ba zai manta da Ganduje ba — Shi ya kai ta matsayin da take kai yanzu,” inji shi.
Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC An ƙayyade maki da shekarun shiga jami’a a NijeriyaAminu ya ba da misali da yadda aka dinga tururuwar shiga APC a lokacin mulkin Ganduje da kuma yadda Gwamnoni suka dinga sauya sheka, wanda ya ce ko hakan ya isa ya nuna kwarewarsa a fagen siyasa.
“A lokacinsa ne karon farko da wata jam’iyyar siyasa a Najeriya ta ga cancantar samar da wata dama da nufin magance matsalar shigar matasa a harkokin siyasa.”
A wani sakon da ya wallafa kafin wasikar, ya ce za su rama biki idan lokaci ya yi, kuma a nan ne za a gane Ganduje shi ne rufin asirin APC.
“Tinubu ya mana rauni sau daya, sau biyu, har sau uku. Allah Ya kai mu ranar ramuwa, ranar da za su gane cewa shi ne rufin asirinsu,” in ji shi.
A bayan nan ne dai tsohon gwamnan na Kano, Ganduje ya ajiye muƙaminsa na shugabancin jam’iyyar APC.
Duk da yake Ganduje ya ce rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus, wasu majiyoyi sun bayyana cewa rikicin siyasa a cikin jam’iyyar ne suka tilasta masa ajiye muƙamisa.
Ganduje ya zama Shugaban APC a watan Agustan 2023, a lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp